Jan 20, 2019 19:12 UTC
  • Mutane 14 Suka Rasa Rayukansu A Wata Gagarumar Gobara A Kasar Faransa.

Majiyar Jami'an tsaro a kasar Faransa ta bayyana cewa wata gagarumar gobara ta kashe mutane akalla 14 a wani wuri kusa da kan iyakar kasar da kasar Swizland.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto majiyar manya-manyan jami'an tsaron kasar ta Faransa na cewa gobarar ta auku ne a garin Savoie na kusa da kan iyaka da kasar Swizlanda a yau Lahadi. Kuma gobarar ta cinye manya manyan gine-gine biyu na gidajen mutane. Banda haka akwai wasu mutane 4 wadanda suke cikin mummunan hali a asbiti sanadiyyar Gobarar. 

Har yanzun ba'a san sanadiyar gobarar ba, sannan babu wanda ake tuhuma da tada ita.

A ranar 12 ga watan Janeru da muke ciki ma an yi wata gobarar a birnin Paris inda a nan ma mutane da dama suka rasa rayukansu ko suka ji rauni sanadiyar gobarar. 

Tags