Feb 01, 2019 19:13 UTC
  • Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Kafa Sabuwar Gwamnati A Kasar Lebanon

Jami'an Siyasa na tarayyar Turai sun yi maraba da kafa gwamnati a kasar Lebanon.

Majiyar muryar JMI ta nakalto Jami'a mai kula da lamuran harkokin waje na tarayyar Federica Mogherini tana fadar haka a yau Jumma'a. Mugareni ta kara da cewa tarayyar Turai da kuma sauran kasashen duniya sun dade suna sauraron kafuwar gwamnati a kasar Lebanon.

Labarin yana kara da cewa duk da cewa an dau lokaci mai tsawo ana tattaunawa tsakanin yan siyasa a kasar ta Lebanon tun bayan zaben majalisar dokokin da aka gudanar a cikin watan Mayun shekara ta 2018, daga karshe Firai ministan kasar Sa'ad Al-Hariri ya sami nasara kafa gwamnati a kasar.

Jami'ar ta kammala da cewa tarayyar ta Turai a shirye take ta yi aiki tare da sabuwar gwamnatin kasar ta Lebanon. A daren jiya Alhamis ne Firai Ministan kasar ta Lebanon Sa'adul Hariri ya bada sanarwan kafa gwamnatin bayan tattaunawa na lokaci mai tsawo da shugaban kasar ta Lebanin Michel Aoun.

Majalisar ministocin sabuwar gwamnatin dai tana da mamboni 30, sannan mafiyawansu sun fito ne daga kungoyi masu gwagwarmaya na kasar.

Tags