Feb 03, 2019 19:06 UTC
  • Jami'an Yansanda 4 Ne Suka Ji Rauni A Zanga-Zangar Kin Tsarin Jari Hujja A Kasar Faransa.

Rundunar yansanda na kasar Faransa ta bada sanarwan cewa jami'an yansanda 4 ne suka ji rauni a fafatawa da masu zanga-zangar kin jinin tsarin jari hujja a kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar ta Faransa ta nakalto rundunar yansandan kasar ta Faransa UNSA tana fadara haka a yau Lahadi ta kuma kara da cewa, a asabar na 12 a jere da masu kin jinin tsarin jari hujja suke zanga-zanga a kasar yansanda hudu ne suka ji rani.

Labarin ya kara da cewa dansanda daya ya ji rauni a birnin Paris daya kuma abirnin Morlaix sannan daya a birnin Bodo sai kuam daya Nonat. 

Tun ranar 17 ga watan Nuwamban shekara da ta gabata ce masu fada da tsarin jari hujja a kasar Faransa wadanda ake kira masu "Farmalar Ruwan goro" suke gudanar da zanga zanga a duk manya manyan biranen kasar, don tilastawa gwamnatin kasar dawowa daga rakiyar tsarin da ke mutunta masu arziki kadai.

Tags