Feb 06, 2019 06:45 UTC
  • Majalisar Dokokin Kasar Faransa Ta Amince Da Wata Doka Ta Murkushe Yan Adawa

Majalisar dokokin kasar Faransa a jiya Talata ta amince da wata doka ta murkushe wadanda suka kira masu tada hankali.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar dokokin wacce yan jam'iyyar shugaban kasa Emmanuel Macron suka fi rinjaye sun amince da dokar da babban rinjaye. 

Yan majalisa 387 ne suka amince da dokar a yayinda 92 kacal suka yi watsi da iata.

Sabuwar dokar ta murkushe yan adawa dai ta bawa yansanda karin dama na amfani da karfi wajen murkushe masu bore,. Har'ila yau dokar ta hana masu zanga -zanga rufe fuskokinsu, banda haka dokar ta takaida 'yencin mutanen kasar Farnsa gaba dayansu.

Tun ranar 17 ga watan Nuwamban da ya gabata ne mutanen kasar Faransa sanye da "Farmala mai launin Ruwan goro" suke zanga zangar kin jinin tsarin jarin hujja wanada ya damu da talaka kaidai a kasar.

 

Tags