Feb 08, 2019 19:15 UTC
  • Wasu Jami'an Kungiyar Tarayyar Turai Sun Bayyana Cewa Britanaya Ce Take Gaba A Hana Sanya Sudia Cikin Kasashen Masu Goyon Bayan Yan Ta'adda.

Wasu jami'an kungiyar tarayyar Turai 3 sun bayyana cewa gwamnatin kasar Britania ce ta kan gaba wajen hana kungiyar sanya kasar saudia cikin kasashen masu bada cin hanci da rashsawa da kuma tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto wadannan jami'an suna cewa mafi yawan kasashen Turai suna jin tsaron a sanya sunan Saudia da kuma Panama cikin jerin kasashen masu tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya da kuma mu'amala da kudade ta hanyar da bata dace ba ne, don tsarin hakan zai shiga matakan da tarayyar zata dauka wadanda ba zasu yi masu dadi ba.

Majiyar ta bayyana cewa kasashen Faransa Jamus Espania da kuma Italya duk suna jin tsaron idan hakan ya faru zasu asarar mai yawa a fagen tattalin arziki. 

A cikin watan Jenerun da ya gabata ne kungiyar tarayyar ta Turai ta fara tattauna batun sanya kasashen Saudia, Panama da kuma wasu kananan Tsibirai a taken Carabian cikin jerin kasashen masu ta'ummu da kudaden haramun kuma suke tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya. 

Amma wadanan manya-manyan kasashen Turai, Musamman Britania suna daga cikin wadanda suke sayarwa kasar Saudia makamai na miliyoyon Euro a ko wace shekara. 

Tags