Feb 09, 2019 17:08 UTC
  • Faransa : Ana Ci Gaba Da Zanga zangar Kyamar Macron

A Faransa, yau Asabar ma masu boren adawa da siyasar shugaban kasar, Emannuel Macron, kan haraji da gazawar gwamnati wajen biyan bukatun masu karamin hali da ya daganci tsadar rayuwa sun sake fitowa kan tituna.

Wannan shi ne karo na 13 da masu boren ke fantsama kan tutina, lamarin dake nuna kasawar shugaban kasar wajen kwantar da hankali.

Masu zanga zangar dai sun ce akwai yiyuwar suyi kira ga wasu manyan kungiyoyin kwadago na kasar domin ci gaba da boren, a yayin da wasu ke kira ga shugaban kasar ya yi murabus.

Rahotannin daga kasar sun ce zanga zanga ta yi muni a yau, inda harma wani daga cikin masu zanga zangar ya rasa hannunsa.

Dama kafin hakan masu zanga zanga sun nuna damuwa akan yadda jami'an tsaro ke amfani da wasu abubuwa masu hadari wajen murkushe boren.

Alkalumman da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar, sun ce mutum sama da mutum 12,000 ne suka shiga zanga zangar ta yau Asabar da misalin karfe biyu na rana agogon wurin, wadanda suka hada da 4,000 a Paris babban birnin kasar, duk da cewa masu zanga zanga na karyata alkalumman mahukuntan wanda suka ce ya kai daruruwa.

Tags