Feb 13, 2019 18:57 UTC
  • Kasashen Jamus, Faransa Da Birtaniya Ba Za Su Halarci Taron Warsaw Ba

Kasashen uku sun bayyana taron da kasar Amurka ta shiyra da cewa yana da illa

Bugu da kari kasashen na Fransa, Jamus da Birtaniya sun ce; Sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya shirya taron ne ba tare da yin shawara ba, don haka sakamako ne na rashin tsari

Jami'an gwamnatocin kasashen uku sun shaidawa cibiyar watsa labaru ta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa "National" cewa; Taron na kasar Poland yana da illoli sannan kuma suka yi suka akan matsayar Amurka dangane da Iran da kuma batun ficewarta daga kasar Syria

A yau Laraba ne Amurka ta shirya gabatar da wani taro a birnin Warsaw na kasar Poland wanda ta bayyana a matsayin na kalublantar Iran, sai dai rashin karbuwarsa ya sa ta sauya masa suna zuwa na gabas ta tsakiya

Tags