Feb 15, 2019 05:32 UTC
  • Indiya Na Cikin Alhini, Bayan Mummunan Harin Kashmir

Hukumomi a Indiya, sun yi allawadai da mummunan harin da ya yi ajalin jami'an tsaron kasar akalla 40 a yankin Kashmir.

Harin da aka kai jiya Alhamis da wata mota da aka danawa bama-bamai, kan wata motar bus ta jami'an tsaron shi ne irinsa mafi muni a yankin cikin shekaru da dama.

Wasu manyan jami'an kasar, sun bi  sahun Fira ministan kasar, Narendra Modi, wajen yin tir da allawadai da harin, tare da aikewa da sakon ta'aziyya ga iyalen wadanda harin ya yi ajalinsu, da kuma fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda harin ya raunana. 

Shi ma dai madugun 'yan adawa na kasar, kana shugaban majalisar wakilan Indiya, Rahul Gandhi, ya yi allawadai da harin.

Tuni dai aka kaddamar da bincike kan harin, musamman ma, kan yadda maharin ya samu wucewa salin-alum gaban jami'an tsaron yankin mai cikaken tsaro da tarin bama-baman da ya kai harin dasu. 

Kungiyar 'Yan ta'adda ta Pakistan, da Jaish-e-Mohammed, ke jagoranta ta dauki alhakin kai harin a cikin wani sakon faifan bidiyo data fitar.

Jaish-e-Mohammed, wanda kasashen yamma suka sanya cikin jerin manyan 'yan ta'adda na duniya, kasar ta Indiya na zarginsa da kai hare hare biyu kan sojojin kasar a cikin shekara 2016.
 

Tags