Feb 21, 2019 06:53 UTC
  • Firai Ministan Britania Ta Bada Sanarwan Samun Ci Gaba A Tattaunawar Brexit

Firai Ministan kasar Britania Theresa May ta bada sanarwan cewa an sami ci gaba a tattaunawan da ta gudanar da shugaban kungiyar tarayyar Turai a birnin Brussel na kasar Beljika cibiyar tarayyar a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Theresa May tana fadar haka a jiya bayan tattaunawa da shugaban kungiyar ta EU, ta kuma kara da cewa batun gabatar da gwara na shari'a dangane da kan iyakar kasar Britania na kasar Island bayan ficewar Britania daga kungiyar yana da matukar muhimmanci. 

A shekara ta 2016 ne mutanen kasar Britania suka zabi ficewa daga tarayyar Turai da karamin rinjaye a wani zaben raba gardaman da aka gudanar a kasar. 

Gwamnatin kasar ta Britania tanada lokaci har zuwa ranar 29 ga watan Maris mai zuwa na ta kammala dukkan shirye-shiryen ficewa daga kungiyar tarayyar ta Turai wanda aka fi saninsa da Brexit.

Majalisar kasar ta Britania ta ki amincewa da yerjejeniya ta farko wacce firai ministan ta cimma da tarayyar ta Turai dangane da shirin ficewar kasar daga kungiyar. 

Tags