Feb 25, 2019 10:13 UTC
  • Shugaban Iraki Ya Fara Ziyara A Faransa

Shugaban kasar Iraki, Barham Saleh, ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Faransa.

Mista Saleh, zai gana da takwaransa na faransa Emanuel Macron, inda bangarorin buyu zasu tattauna kan batutuwan da suka shafi hulda tsakanin kasashen biyu ta fuskar tsaro da kuma kasuwanci.

Ana sa ran kuma kasashen biyu zasu tattauna kan makomar mayakan dake ikirari da sunan jihadi ‘yan asalin kasar ta Faransa da har yanzu suke a yankin.

Ko baya ga hakan bangarorin zasu tabo batun sake Iraki da kuma tattalin arziki.

 

Tags