Feb 25, 2019 15:12 UTC
  • Mutanen Da Suka Mutu A India Sanadiyar Kwankwanar Barasa Mai Guba Ya Kai 150

A kalla mutane 150 ne suka mutu sanadiyyar shan barasa a arewa maso gabacin kasar India, karo na biyu kenan a cikin wata guda.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa rahotanni da suke fitowa daga asbitoci uku a lardin Assam sun nuna cewa wasu mutane 170 suke jinya a yayinda har yanzun ana kawo masu karin wadanda annobar ta shafa.

Majiyar hukumomi a lardin sun nuna cewa jami'an tsaron kasar sun bincike don gano asalin inda barasar ta fito, don hukunta wadanda suka harhadata. 

Har'ila yau labarin ya kara da cewa an aika da samfurin gubar da ta halata mutanen zuwa dakunan gwaje-gyaje don gano irin nau'in guban da aka hada barasar da shi. 

A jiya asabar dai an ce mutane 84 suka rasa rayukansu sanadiyar shan giyar. 

 

Tags