Feb 28, 2019 18:33 UTC
  • Shugaban Amurka Ya Kasa Cimma Yarjejeniya Da Koriya Ta Arewa

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa ya kasa cimma yerjejeniya da tokoransa na korea ta Arewa Kim Jon Ung bayan tattaunawa na kwanaki biyu a birin Hanoi, babban birnin kasar Vietnam.

 

Trump ya bayyana haka ne a yau Alhamis a wani jawabin da yayiwa yan jaridu bayan sun kawo karshen taron nasu ba tare da cimma wata yerjejiya ba, ya kuma kara da cewa Korea ta Arewa tana bukatar Amurka ta dage dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata.

Trump ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ba shirye take da dage dukkan takunkuman da ta dorawa kasar Korea ta Arewa ba, sai dai kuma ba ta tunanin kara kakaba mata wasu Karin takunkumi ba.

A wani bangaren na jawabinsa ga amsoshin yan jaridu, shugaban ya ce zai ci gada rike kekyawar dangantakar da ke tsakaninsa na shugaba Kim Un Yung, don ya yi masa alkawarin cewa korea da Arewa ba za ta sake gwajin makamanta na nukliya ko masu linzami ba.

Har’ila yau shugaba ya ce basu tsaida wani lokaci na sake haduwa da shugaba Kim Un yung ba.

 

 

Tags