Mar 03, 2019 07:33 UTC
  • An Kara Kashe Wasu Mutane 8 A Yakin Pakistan Da India

A sabon fada da ya barke ya yakin da kasashen India da Pakistan suke yi, an kashe mutane 8

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a bude wutan da sojojin India suka yi a daren jiya Asabar sojojin kasar Pakistan 2 ne suka kwanta dama. Majiyar sojojin kasar Pakistan ta kara da cewa barin wutan sojojin India ya kashe wani yaro, sannan wasu mutane 3 sun ji rauni a yankin Kashmir da ke bangaren Pokistan.

Majiyar ta kara da cewa a maida martanin da sojojin Pakistan suka yi, yara guda biyu da mahaifiyansu sun mutu sannan mahaifinma ya ji rauni a yankin Poonch na lardin kashmir da ke karkashin ikon kasar Indiya. 

Yaki ya barke tsakanin kasashen India da Pakistan ne bayan da wasu boma-bomai suka tashi a yankin Kashmir da ke karkashin ikon kasar Indiya a ranar 14 ga watan Fererun da ya gabata, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar India 40.

Daga nan ne kasar India ta kai hare-hare da jiragen saman yaki a kan wuraren da ta kira sansanin yan ta'adda a cikin kasar Pakistan, inda ta kashe mutane da dama.

 

Tags