Mar 07, 2019 15:53 UTC
  • EU Na Fatan Venezuela, Zata Canza Tunani Kan Korar Jakadan Jamus

Kungiyar tarayya Turai ta (EU), ta ce tana fatan kasar Venezuela zata canza tunani kan korar jakadan jamus daga kasar.

Da take sanar da hakan, babbar jami'ar harkokin kasashen waje ta kungiyar ta EU, Federica Mogherini, ta ce basu ji dadin matakin ba, duk da cewa suna kan matsayin na ci gaba da tattaunawa da dukan bangarorin na Venezuella.

A jiya ne dai gwamnatin Nicolas Maduro ta sanar da korar jakadan na Jamus a kasar, Daniel Kriener, tare da dibar masa wa'adin sa'o'i 48 na ya fice daga kasar, bisa zarginsa da shishigi a cikin al'amuran cikin gidan kasar.

Jakadan na Jamus yana daga cikin jakadun kasashen waje da ke birnin Caracas wadanda kuma suka tarbi jagoran 'yan hammaya na kasar ta Venezuela, Juan Guaido, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na riko, a filin jirgi sama na Caracas bayan ya dawo daga ziyarar da ya kai a wasu kasashen yankin.

Tags