Mar 12, 2019 05:47 UTC
  • Amurka Taki Amincewa Korea Ta Arewa Ta Kakkabe Makamanta mataki-Mataki

Wakilin Amurka a harakokin da suka shafi al'amuran korea ta Arewa ya bayyana cewa Washington na adawa da kakkabe makaman nukiyar kasar Korewa ta arewa a mataki-mataki

kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto Stephen Biegun wakilin  Amurka na musaman kan al'amuran da suka shafi kasar korea ta Arewa a wannan Litinin na cewa Washington na adawa da shawarar da kasar korea ta bayar na lalata makaman Nukiyar kasarta a mataki- mataki.

Wakilin na Amurka kan al'amuran da suka shafi kasar Korea ta Arewa ya kara da cewa bayan dage takunkumi, Amurka na iya yiwa kasar Korea tayin wasu ababe da dama da za su amfanar da kasar.

Bayan gudanar da zama biyu ba tare da cimma matsaya ba, mista Stephen Biegun ya ce akwai yiyuwar sake zama tsakanin shugabanin kasashen biyu, to saidai hakan ya danganta da shawarar da Shugaba Trump ya yanke.

Ya zuwa yanzu, so biyu shugabanin kasashen Amurka da Korea ta Arewa wato Donal Trump da Kin Jong-un suna zama domin cimma matsaya kan batun Nukiliyar kasar Korea ta arewa ba tare da cimma matsaya ba.

Shugaba Kin Jong-un dai ya sha sukan mahukuntan kasar Amurka, sanadiyar matsin lambar tattalin arziki da suke yi kan kasarsa.

Tags

Ra'ayi