Mar 12, 2019 07:56 UTC
  • Amurka Ta Bukaci Boeing, Ya Aiwatar Da Canji A Samfarin Jirgi 737 MAX 8

Mahukuntan Washington sun ce zasu dauki matakai, biyo bayan hatsarin jirgin saman fasinja na kamfanin Ethiopian Airlines Kirar Boeing 737 MAX 8.

A yanzu Amurka ta bukaci kamfanin na Boeing da ya aiwatar da wasu gyare gyare a jiragen, amma ba tare da dakatar da aiki dasu ba.

Wannan dai ya biyo bayan da wasu kasashen duniya suka fara daukan matakin jingine aiki da samfarin jirgin kirar Boeing 737 MAX 8, da Amurka ke kerawa.

Sanarwar da hukumar sufirin jiragen sama ta FAA, ta fitar tace a shirye take ta dauki matakai wadanda suka dace kuma cikin gajaren lokaci, bayan hatsarin jirgin na Ethiopian Airlines Kirar Boeing 737 MAX 8, da ya yi ajalin mutum 157 a ranar Lahadi data gabata.

A halin da ake ciki dai, hannayen jari na kamfanin Boeing sun fadi da kashi 12% a baya baya nan.

Kasashen China, Ethiopia da kuma Indonesia, su ne sahun gaba wajen daukar matakin jingine aiki da jiragen samfarin Boeing 737 MAX 8, wanda shi ne jirgi mafi samun karbuwa a kasuwannin duniya.

Tags

Ra'ayi