Mar 13, 2019 05:41 UTC
  • Fox News Ta Nisanta Kanta Daga Furucin Cin Mutuncin Hijabi

Tashar talabijin ta Fox News ta kasar Amurka ta nisanta kanta daga wani furuci da wata ma’aikciyar tashar ta yi da ke cin zarafin 'yar majalisar dokokin Amurka musulma saboda saka lullubi da take yi.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto, tashar ta Fox News ta bayyana furucin ma'aikaciyar da cewa ra'ayinta ne na kashin kanta, amma ba ra'ayin tashar ne ba.

Ma'ikaciyar tashar ta Fox News ta yi kakkausar suka kan yadda 'yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Umar take shiga cikin majalisar da lullubi irin na addinin musulunci a kanta, inda ta bayyana hakan da cewa ya sabawa dokokin Amurka.

Wannan dai na daga cikin irin kalamai na tsangwama da Ilhan Umar take fuskanta daga bangarori daban-daban na masu adawa da ita a cikin kasar ta Amurka, musamman kasantuwarta bakar fata kuma musulma.

 

Tags

Ra'ayi