Mar 15, 2019 09:08 UTC
  • Koriya Ta Arewa Na Tunanin Soke Tattaunawar Nukiliyarta Da Amurka

Kasar Koriya ta Arewa ta ce tana tunanin dakatar da tattaunawar data fara da Amurka kan batun nukiliyarta, bayan da tattaunawa ta tsakanin shuwagabannin kasashen biyu ta watse ba tare da cimma wata matsaya ba.

Da yake sanar da hakan karamar ministan harkokin waje na Koriya ta Arewar, Choe Son Hui, ta ce basu da niyyar mika kai ga bukatar Amurka, sannan kuma bama shirye wajen shiga irin wannan tattaunawar.

A karshen watan fabarairu da ya gabata ne, shugaba Donald Trump na Amurka da kuma takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, suka yi ganawa ta biyu a birnin Hanoi, inda kuma suka tashi baran-baran ba tare da cimma wata mastaya ba.

A yayin zantawa ta wayar tarho da shugaban Korea ta Kudu, Moon Jae-in, shugaba Trump ya ce, ya yi nadamar rashin cimma wata matsaya da Kim Jong-un bayan tattaunawar da ta gudana a tsakaninsu.

Sai dai wata sanarwa da fadar gwamnatin Korea ta Kudu ta fitar, ta ce, Trump din ya nuna aniyar warware batun na Korea ta Arewa ta hanyar sake shirya wata tattaunawa da kasar.

Tags