Mar 17, 2019 05:33 UTC
  • Zanga Zangar Faransa Na Kamari

Rahotanni daga Faransa na cewa zanga zangar da masu dorawar riga keyi, na ci gaba da kamari, inda a jiya Asabar masu boren suka kona shaguna tare da kwasar ganima a babban titin ''Champs-Elysées'', na Paris babban birnin kasar.

Bayanai sun ce a wasu wuraren birnin anyi artabu tsakanin jami'an tsaro, da masu zanga zangar.

Kimanin mutane 7,000 zuwa 8,000 suka shiga zanga zangar a tsakiyar ranar jiya Asabar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Christophe Castaner, ya yi tir da lamarin, yana mai baiwa mahukuntan birnin dasu dauki kwararen matakai na dakile irin wannan ta'asar ta bata gari dake fakewa da masu zanga zangar.

A wannan Asabar dai an shiga mako na 18 da boren da jama'ar kasar keyi na kin jinin manufofin gwamnatin shugaba Emanuel Macron, musamman kan batun haraji da ci gaba da yin burus da bukatun masu karamin hali.

 

 

Tags