Mar 19, 2019 14:57 UTC
  • Zanga Zangar Faransa : An Kori Shugaban 'Yan Sandan Birnin Paris

Piraministan kasar Faransa, Edouard Philippe, ya sanar da korar shugaban 'yan sanda birnin Paris, biyo bayan mummunar zanga zangar da masu bore a kasar da aka fi sani da masu dorawa riga, sukayi a ranar Asabar data gabata.

M. Philippe, ya ce za'a canza shugaban 'yan sanda birnin na Paris,  Michel Delpuech, a ranar Laraba mai zuwa a taron majalisar ministocin kasar, inda shugaba Emanuel Macron zai sanar da nadin sabon shugaban 'yan sanda na Paris, Didier Lallement.

Sabon shugaban 'yan sanda da za'a nada shi ne tsohon sakatare janar na ma'aikatar cikin gidan kasar, kuma zai maye gurbin M. Delpuech, wanda aka ambato a cikin wata harka ta rashin daidaita al'amuran tsaron jama'a yadda ya kamata a babban birnin kasar. 

A ranar Asabar data gabata boren da masu dorawar riga keyi, ya ci gaba da yin kamari, inda masu zanga zangar suka kona shaguna tare da kwasar ganima a babban titin ''Champs-Elysées'', na Paris babban birnin kasar.

Baya ga hakan kuma bayanai sun ce a wasu wuraren birnin anyi artabu tsakanin jami'an tsaro, da masu zanga zangar.

A halin da ake ciki dai hukumomin kasar ta Faransa na nan na nazarin matakan da zasu dauka na shawo kan masu zanga zangar a yayin da aka shiga mako na 18 da boren, da jama'ar kasar keyi na kin jinin manufofin gwamnatin shugaba Macron, musamman kan batun haraji da ci gaba da yin burus da bukatun masu karamin hali.

Tags