Mar 20, 2019 08:54 UTC
  • China ta Kame Musulmi Kimanin Dubu 13 Da Yaki Da Ta'addanci

Gwamnatin kasar China ta sanar da kame wadanda ta kira 'yan ta'adda kimanin dubu 13 a yankunan musulmin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar China ta fitar da rahoto da ke cewa, daga shekarar 2014 zuwa wannan shekara da muke ciki ta 2019, an kame 'yan ta'adda kimanin dubu 13 a cikin yankin Sin Kiyang na mabiya addinin muslucni.

Bayanin na gwamnatin China ya ce, dukkanin mutanen da aka kama dai an same su ne da aikata wasu ababen da suka sabawa dokokin kasar, musamman wadanda suke da alaka da ta'addanci, inda bayanin ya ce an kame mutane 12, 995 bisa zarginsu da ayyukan ta'addanci, yayin da kuma aka ladabtar da wasu kimanin dubu 30, bayan samunsu da aikata ayyukan da suka shafi addini ba tare da iznin gwamnati ba.

Gwamnatin kasar China dai ta fitar da wannan sanarwa ce dai sakamakon kakkausar suka da take sha daga kungiyoyin kare hakkin bil daga sassan duniya, kan yadda take takura ma musulmi marassa rinjaye a kasar, inda a halin yanzu gwamnatin kasar take kokarin danganta musulmi kasar da ayyukan ta'addanci, domin samun hujjar gallaa musu.