Mar 21, 2019 09:51 UTC
  • Faransa Ta Nuna Adawarta Da Dage Ficewar Birtaniya Daga Cikin Kungiyar Tarayyar Turai

Faransar ta ce ba za ta amince da bukatar Birtaniyar ba har sai ta samu tabbacin cewa 'yan majalisar kasar Birtaniyar za su amince da ficewar Birtaniyar daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto Jean-Yves Le Drian ministan harakokin wajen Faransa na cewa idan a nasu mahukuntar birnin Paris sun amince da bukatar Birtaniyan to wajibi ne kasar ta Birtaniya ta rufe idanuta a game da zaben watan Mayu da ake shirye-shriyen gudanarwa.

Le Drian ya bayyana hakan ne a wannan laraba, bayan da Firaministar kasar Theresa May ta sake mika bukata ga shugabannin kungiyar Tarayyar Turai wato EU, na tsawaita wa'adin ficewar kasarta daga kungiyar zuwa ranar 30 ga watan Yunin bana.

Birtaniya ta mika bukatar a wannan Laraba a Brussels babban birnin kasar Beljiyam, a jajibirin taron kolin da kungiyar za ta yi. 

A nasa bangare, shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, ya ce ana iya bai wa Birtaniya karin wani takaitaccen lokaci na jinkirta ficewarta daga kungiyar kasashen, bisa sharadin samun goyon bayan majalisar kasar.

A wannan  Alhamis ne ake sa ran majalisar Turan za ta tattauana batun daga cikin batutuwan da ke a gabanta lokacin taron na koli.

Tags