Mar 21, 2019 09:53 UTC
  • Guteress Ya Taya Al'ummar Iran Murnar Noruz

Saktare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya taya al'ummar kasashen dake bikin Noruz murna

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Antonio Guteress saktare janar na MDD cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a wannan alhamis yana cewa ranar sallar Noruz, dama ce na sake sabunta jagoranci domin ci gaban Duniya kuma muna taya duk al'ummar kasashen da suke bikin wannan rana.

A shekarar 2009 ne aka girmama ranar Noruz a matsayin al'adar wasu kasashe tare da sanya ranar cikin kundin al'adu na Dan Adam.

A shekarar 2010 Majalisar Dinkin Duniya bisa shawarar wasu kasashe kamar Iran da Azarbaijan da Afganistan da Indiya da sauransu, ta amince ta bayyana ranar a matsayin ranar Noruz ta Duniya.