Mar 22, 2019 07:30 UTC
  • Tarayyar Turai Ta Ki Yarda Da Tabbatar Da Ikon 'Isra'ila' A Kan Tuddan Golan Na Siriya

A wani abu da ake ganinsa a matsayin fito na fito da Amurka, kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da rashin amincewarta da tabbatar da ikon haramtacciyar kasar Isra'ila a kan tuddan Golan na kasar Siriya.

A rahoton da ta watsa, tashar talabijin din Rusiyal Yaum ta kasar Rasha ta ce jiyo Maja Kacijancic, kakakin babbar jami'ar harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turan, Federica Mogherini, tana fadin hakan inda ta ce: Matsayar tarayyar Turai dai kan waye ya mallaki Tuddan na Golan bai sauya ba.

Maja Kacijancic ta ci gaba da cewa bisa dokokin kasa da kasa dai, kungiyar Tarayyar Turai ba ta yarda da ikon haramtacciyar kasar Isra'ila a kan yankunan da ta mamaye a shekarar 1967 ba cikinsu kuwa har da Tuddan na Golan, tana daukar wadannan wajajen ne a matsayin wajejen da 'Isra'ilan' ta mamaye su.

A jiya Alhamis ne dai shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa lokaci yayi da Amurka za ta amince a hukumance da ikon 'Isra'ila' a kan tuddan na Golan na kasar Siriya, lamarin da ya fuskanci rashin amincewa daga wajen kungiyar kasashen Larabawa, Turkiyya da kuma Rasha.

Tags