Feb 02, 2016 15:18 UTC
  • HKI
    HKI

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi ba ya bata shirin da ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako inda muke amsa tambayoyin da kuka aiko mana ta hanyoyin da kuka saba saduwa da mu. To yau ma dai ga mu da wani sabon shirin da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkonsa har zuwa karshensa. Tambayar mu ta farko ta fito ne daga mai sauraren mu Laraba Tabawa Dahiru, Zaria Nigeria wacce take cewa ina son ku yi min karin

To Malama Laraba Tabawa mun gode kwarai da gaske da wannan tambaya taki da fatan kina cikin koshin lafiya. Sai ki gyara zama don sauraren abin da muka tanadar miki. Sanannen abu ne cewa a kasashe daban-daban na duniya, akwai kamfanoni da wasu hamshakan masu kudi da jami'an gwamnatoci da suke taimakawa da dukkan abin da ya sawwaka gare su wajen ci gabantar da kungiyar yahudawa ta duniya gaba da daure musu gindi wajen ci gaba da ayyukan ta'addancin da suke yi wa kasashen musulmi musamman ma dai al'ummar Palastinu marasa kariya. Babu kokwanto cikin cewa idan da ba don irin wannan goyon baya ba, to da yahudawan ba su ci gaba da cin karensu babu babbaka ba akan wadannan al'ummomi. Don haka irin wadannan kamfanoni da kike son sani a gaskiya suna da yawan gaske ta yadda ba za mu iya kawo su a wanann fili ba saboda karancin lokacin da muke da shi. Sannan abu na biyu kuma shi ne cewa, saboda irin kiyaye sirri da yahudawan suke da shi wajen gudanar da ayyukansu, abu ne mai wahalan gaske ko kuma a ce abu ne da ba zai yiyu ba a iya gano dukkan sunayen kamfanoni da mutanen da suke da alaka da su. To sai dai kawai za mu dan iya yin ishara ne da wasu abubuwa kawai don dai a fahimci lamarin da kyau amma dai ina ana son karin bayani sosai a na iya komawa ga sannannen littafin nan da aka buga a shekarar 1998 mai suna "The Secret of Jews Lobby In The World" wanda ya yi karin bayani kan kamfanoni na kudi, kasuwanci da masana'antu na kasa da kasa wadanda ko dai mallakan yahudawa ne ko kuma suna da bakin magana cikinsu. Yana da kyau a san cewa wadannan kamfanoni na yahudawan ko kuma wadanda suke da alaka ta kut da kut da su kamfanoni da suke gudanar da ayyukansu a fagage daban-daban da suka hada da sufuri da zirga-zirga, akwai kuma wasu kamfanonin da suke gudanar da ayyukansu a bangarorin kere-kere da harkokin na'ura mai kwakwalwa wadanda suke da muhimmancin gaske ga yahudawan, hakan kuwa saboda samar da sabbin na'urori na sadarwa da ake ta yi a bangare guda kuma ga irin tasirin gaske da wannan bangare yake da shi a fannin tattalin arziki da kuma leken asiri. Don haka ne tun bayan kafa HKI yahudawa sun ba da himma wajen zuba jari a wadannan fagage ta yadda za su kasance sama da dukkan kasashen larabawa a wannan bangare. Baya ga hakan kuma, akwai wasu hanyoyin da suke bi wajen ganin sauran al'ummomi musamman na laraba da musulmi ba su samu ci gaba a wannan bangare ba. Daga cikin irin wadannan hanyoyi kuwa har da kashe kwararru da masanan wadannan kasashe ko kuma masanan da suke taimaka musu wajen cimma samun ci gaba a bangaren kere-kere kamar yadda ya faru cikin 'yan watannin nan a kasar Iran inda ake zarginsu da hannu cikin kashe wasu fitattun masanan kasar Iran. Abu na biyu kuma shi ne matsin lamba da hana kasashe da gwamnatocin hana zuba jari a irin wadannan kasashen da kuma barazanar kaiharin soji akan irin wadannan kamfanoni da masana'antu babban misalin hakan shi ne irin barazanar da suke yi wa cibiyoyin nukiliyan zaman lafiya na Iran da kuma hare-haren da suka kai a baya a irin wadannan wajaje a kasashen Iraki da Siriya da sauransu. Wato a takaice dai duk wani fage na kasuwanci da kuma hanyoyin samun kudade ko kuma tasiri na fadi a ji a duniyan nan da yahudawan ba su shige shi ba, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar tusa 'yan koransu a wajen wadanda za su lamunce musu bukatar da suke da ita. Malama Laraba Tabawa wannan dai shi ne abin da za mu iya gaya miki dangane da wannan tambaya taki don kuwa kamfanunan suna da yawan gaske shi yasa ba za mu iya kawo su ba, amma dai mai son karin bayani yana iya neman wannan littafin da muka ambata a baya. Mun gode.

Tags