Feb 02, 2016 15:23 UTC
  • Haramtacciyar Kasar Israila
    Haramtacciyar Kasar Israila

Yanzu kuma bari mu je ga tambayar mu ta biyu a cikin wannan shirin wacce ta fito daga mai saurarenmu Malam Sirajo Ammani daga Yola jihar Adamawan Nigeria wanda yake cewa don Allah ku yi min karin bayani dangane da dalilin da ya sanya shugabannin Amurka musamman 'yan mazan jiyan da suka kafa gwamnati a kasar a baya-bayan nan suke mika kai ga yahudawa dari bisa dari.

To Malam Sirajo mun gode da wannan tambaya taka da fatan kana cikin koshin lafiya. Ga abin da muka tanadar maka. To dangane da wannan tambaya taka dai a hakikanin gaskiya akwai dalilai da yawa kuma masana sun yi bayani kansu, to amma mafi yawa daga cikin masanan musamman cikin shekarun nan sun fi ba da muhimmanci kan batutuwa guda biyu wato maslaharsu da kuma akida. Dangane da batun maslaha dai ana iya cewa wanann maslahar ta shafi bangaren dukiya ne ko kuma bangaren son mulki da kuma juya duniya yadda suke so da dai sauransu wadanda ta kowane guda daga cikin wadannan abubuwa za a iya ganin cewa bangarorin biyu sun yi tarayya cikin hakan. Batu na biyu kuma wanda za mu fi ba shi muhimmanci a nan shi ne batun akida. Da farko dai cikin 'yan shekarun da suka gabata din nan a kasar Amurkan an sami bayyanar wasu 'yan siyasa a Amurkan wadanda kuma sun sami shiga da tsoma baki cikin harkokin gudanarwa na kasar da suke da wata akida wacce ta samo asali daga darikar nan ta Protestant. Su dai wadannan 'yan mazan jiya da suke da sunaye da kungiyoyi daban-daban sun fito fili da kuma samun wannan karfi ne a shekarun 1970, don kuwa ayyukansu ya sami karfi da fitowa fili ne a shekarar 1976 lokacin da suka ba da gagarumar goyon bayansu ga Jimmy Carter dan takaran shugabancin Amurkan a wancan lokacin wanda kuma daga baya ya kasance shugaban kasar.


Hakan kuwa ya faru ne saboda shi kansa Carter yana daga cikin mutane masu tsananin kishin addinin Kiristanci sannan kuma yana ganin kansa ne a matsayin mutumin da ya tuba daga zunuban da ya aikata ko kuma abin da ake kira da turanci 'born again'. Har ila yau kuma a zaben da aka gudanar a shekarar 1980, wadannan kiristoci sun goya wa Ronald Reagan, dan takaran shugabancin Amurkan a jam'iyyar Republican a wancan lokacin wanda kuma daga baya ya zamanto shugaban kasar, sun yi hakan ne don suna ganin Reagan din a matsayin 'born again' din, kamar yadda kuma wadannan masu tsaurin ra'ayi suka goya wa George W. Bush, saboda suna ganinsa shi ma a matsayin 'born again' din. Haka dai lamarin yake, to sai dai a wannan karon, wato lokacin Bush din wadannan kiristoci sun fi samun bakin magana da kutsawa cikin harkokin gwamnati sama da lokutan da suka wuce saboda irin ba su dama da Bush din ya yi na su yi hakan saboda shi ma yana ganin kansa a matsayin mai riko da addinin kirista sau da kafa. Duk wadanda suka karanci irin akidu da tunanin wadannan kiristoci masu tsaurin ra'ayi za su gano irin mugun akidar da suke da ita na son amfani da karfi, tursasawa, gaba da Musulunci da dai sauransu. Irin wannan akida ta su ce ta sanya suka raba duniya gida biyu, wato alheri da sharri, inda suke ganin kansu a matsayin wadanda suke tare da alheri da kuma tafarkin tsira sauran mutane kuma da ba sa tare da su su ne masharranta masu bakar aniya. A fili muna iya ganin wannan akida cikin bayanan da shugaban Amurkan Bush ya dinga yi a baya, inda ya raba duniya gida biyu, masu alheri da ma'abuta sharri, wato duk wanda yake tare da su kuma ya amince da abin da suke so to wannan shi ne ma'abucin alheri wanda kuma ya ki amincewa da akidu da ra'ayinsu shi ne ma'abucin sharri, hakan ne ma ya sanya ya kira wadansu kasashe uku wato Iran, Iraki da Koriya ta Arewa a matsayin "Kusurwoyin Sharri' ko kuma 'Axis of Evil'.

Daya daga cikin bangare mafi muhimmanci da ke jawo kace nace (wanda kuma yake da alaka da batun da muke yi a wannan shiri) shi ne akidar nan ta Karshen Duniya da abubuwan da za su faru a lokacin. Wadannan kiristoci dai sun yi amanna da cewa karshen duniya dai ya zo saboda kusan dukkan alamomi sun bayyana wadanda ma suka rage suna kan hanya, kamar yadda da dama daga cikin jagororin wadannan mutane suna ganin harin 11 ga watan Satumban 2001 a matsayin wani lamari da ya share fagen zuwan karshen duniya. To su dai wadannan mutane sun yi tarayya da yahudawan sahyoniya din a cikin daya daga cikin akidarsu ta cewa kafin bayyanar Annabi Isa al-Masihu (a.s) dole ne yahudawa su yi hijira zuwa kasar Palastinu da mamaye kasar, wannan akida dai ita ce ta sanya wadannan kiristoci 'yan mazan jiya suke nuna goyon bayansu dari bisa dari ga yahudawan sahyoniya wajen mamaye kasar Palastinu da ci gaba da zama a wajen. Wadannan 'yan mazan jiya sun yi amanna ne da cewa bayan mamaye kasar Palastinu, dole ne yahudawa su ruguza masallacin Al-Aksa da gina wani wajen ibadansu a madadinsa, bayan haka kuwa yaki zai barke mai tsananin gaske daga nan ne Dujal ko kuma wanda suka kira 'Anti Christ' (makiyin almasihu) zai bayyana. Bayan bayyanar Dujal ba da jimawa ba Isa al-Masihu zai bayyana inda zai yafe wa kiristoci zunubansu da kuma daukansu zuwa sama don su tsira daga dukkan fitinun da ake ciki a duniya. A daidai wannan lokaci da ake ci gaba da rikici, sannan kuma Dujal ya kama hanyar samun nasara ne Annabi Isan zai sauko kasa don fada da Dujal da kawar da shi, to daga nan ne mulkinsa na shekara dubu zai fara. To wannan akida ita ce ta hada su. Wato a bangare guda su yahudawa za su sami biyan bukatarsu ta mamaya su kuma za su sami abin da suka kira ceto. To Malam Sirajo a takaice wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da wannan tambaya taka da fatan ka gamsu. A huta lafiya.

-----------------------------

END

Tags

Ra'ayi