Feb 02, 2016 15:27 UTC
  • Kallafaffen yakin Iran da Iraki
    Kallafaffen yakin Iran da Iraki

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Matambayi Ba Ya Bata shirin da ke amsa muku tambayoyin da kuka aiko mana wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako. To yau ma dai ga mu da wani sabon shirin inda za mu amsa muku tambayoyin da kuka aiko mana.

 Idan dai masu saurare ba su mance ba a shirin mu da ya gabata mun amsa tambayar farko da muka samu daga wajen mai sauraren mu Odita Janar Muhammadu Gande Faya Sabis P.O.Box 1697, Sokoto State, Nigeria wanda ya ke son karin haske dangane da dalilan yakin Iran da Iraqi, inda a makon da ya wuce din muka amsa masa tambayarsa ta farko mu ka ce ta biyun kuma sai a wannan makon. To da yardar Allah za mu yi kokarin amsa masa tambayar tasa ta biyun a yau duk kuwa da cewa tana bukatar lokaci. Don haka sai a biyo mu sannu a hankali:

-----------------------------------------

Masu saurare barkanmu da sake saduwa. To Odita Muhammadu Gande, dangane da dalili ko kuma dalilan wannan yaki na shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki, masana daban-daban sun yi bayani kan dalilan hakan, to sai dai kuma akwai wadansu abubuwa da kusan dukkaninsu suka yi tarayya a kansa a matsayin dalilin yakin wanda a nan gaba za mu gani. Da farko dai bari mu kawo ra'ayin wasu daga cikin masana da 'yan siyasa na kasashen yammaci da na larabawa kan dalilin yakin sannan kuma daga karshe mu rufe da yadda jami'an Iran suke ganin hakikanin dalilin wannan yakin da aka kallafa wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran din na tsawon shekaru 8. To amma yana da kyau a fahimci cewa mun kawo wadannan ra'ayuyyuka na masanan kasashen yammacin ne don kara irin masaniyar da muke da ita, to amma ko da wasa ba wai mun amince da dukkanin abin da suka fadi din ba ne a matsayin dalilin yakin. A matsayin misali James Bill sanannen masanin ilmin siyasa na jami'ar Virginia ta Amurka yana ganin dalilin yakin shi ne kokari ne na samun iko a yankin Tekun Fasha yana mai cewa Saddam dai yana son samun karfi ne na siyasa wannan yankin da kuma kawo karshen juyin juya hali na Iran wanda yake ganinsa a matsayin barazana ga yanayi siyasa na yankin. Shi kuwa tsohon shugaban Amurka Richard Nixon yayin da ya ke magana kan dalilan yaki ya yi ishara ne da siyasar Amurkan a kafin da kuma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda ya ce siyasar Amurka a shekarun 1970 shi ne amfani da Iran wajen kawar da irin akidar gurguzu da ke iko a Iraki, sannan a shekaru 1980 kuwa (wato bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran) siyasar Amurkan ita ce amfani da Iraki wajen kawar da juyin juya halin Musulunci na Iran. Shi kuwa Anthony Carldzman shugaban cibiyar binciken na siyasar Amurka sannan kuma daya daga cikin masana harkokin soji na kasar ya bayyana dalilai na kabilanci da 'yan kasanci da kuma rikici na kan iyaka a matsayin dalilin wannan yakin. Sannan kuma daga karshen bayaninsa ya bayyana cewar Saddam da mukarrabansa sun yi imanin cewa matukar suna son samun iko a yankin Tekun fasha to wajibi ne su dau matakin amfani da karfi wajen kawo karshen sauyin da aka samu a Iran a wancan lokacin (wato nasarar juyin juya halin Musulunci). Shi ma Graham Fuller marubuci sannan kuma tsohon jami'an kungiyar leken asirin Amurka CIA shi ma ya bayyana wadannan batutuwa na kabilanci da tarihi da kan iyaka a matsayin wasu daga cikin dalilan yakin, to sai dai shi ma bai boye cewa nasarar juyin juya halin Musulunci da aka samu a kasar Iran ya sauya yanayin wannan yanki na gabas ta tsakiya, yana mai cewa wajibi ne a yi la'akari da hakan yayin da ake sharhi kan dalilan faruwar wannan yakin.


Shi ma a nasa bangaren Abu Ghazala, tsohon ministan tsaron kasar Masar a lokacin yakin ya bayyana cewar yaki tsakanin Iran da Iraki yaki ne tsakanin larabawa da farisawa wanda yake da tsohon tarihi. Baya ga wannan sharhi, Abu Ghazalan ya kara da cewa ko shakka babu nasarar da juyin juya halin Musulunci ya yi a kasar Iran lamari ne da ya sauya lamurra da kuma irin mizanin karfi da ake da shi a yankin Tekun Fasha, don haka ya ce harin da Iraki ta kai wa Iran wani kokari ne na tabbatar da ikonta a wannan yankin musamman bayan faduwar gwamnatin Shah wacce a lokacin take rike da wannan matsayi na zama 'yar sandan yankin Tekun Fashan. Shi ma Efraim Karsh bayahude sannan kuma mai sharhi kan lamurran da suka shafi soji ya bayyana fatan da kasar Iraki take da shi na rarraba kasar Iran a matsayin dalilin wannan yaki yana mai cewa bayan nasarar juyin juya halin Musulunci Saddam Husain dai ya gagara hakuri ci gaba da ganin an sami sauyin akida a Iran wanda hakan sai rage masa irin kutsawar da yake son samu a yankin. Wadannan kadan kenan daga cikin masana 'yan kasashen waje da suka bayyanar da ra'ayinsu kan dalilin wannan yakin. To wani abin da ya kamata a lura da shi cikin kusan dukkanin maganganunsu shi ne cewa dukkaninsu sun yi amanna da cewa kasar Iraki ta kaddamar da wannan yakin ne don kawo karshen irin sauyin da aka samu a wannan yankin sakamakon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran. Wato a takaice dai saboda kawo karshen wannan juyi na Musulunci da bai jima da kafuwa a kasar ba. To hatta sauran mutanen da suka yi magana kan wasu dalilan irin su kabilanci, farisawa da larabawa da sauransu sun bayyana cewar dukkanin wadannan abubuwa wasu lamurra ne kawai da aka fake da su don cimma babbar manufar wacce ita ce kifar da sabuwar gwamnatin Musulunci a kasar Iran.

------------------------------

To masu saurare da Odita Janar Muhammadu bayan mun ji wadannan ra'ayi na masana 'yan kasashen waje wadanda wasun su ma ko kuma gwamnatocin kasashen su suna da hannu wajen ruruta wutan wannan yaki da kuma taimaka wa Saddam da kudade da kuma makamai wajen yakan Iran din, to yanzu kuma kamar yadda muka ce bari mu ji su kuma Iran masana da jami'an Iran ya ya suke ganin dalilin wannan yakin. To a wannan bangaren ma dai masanan Iran da jami'an kasar da dama sun yi bayani kan dalilan yakin, to bisa la'akari da karancin lokacin da shirin na mu yake da shi, za mu yi ishara ne kawai da abin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fadi dangane da wannan batu na dalilin yakin. A wata hira da aka yi da shi a lokacin da ake tsakiyar yaki, an tambaye Ayatullah Khamenei dangane da ra'ayinsa kan dalilin yakin inda ya ke cewa: "Dangane da manufa da kuma dalilan da suka sanya gwamnatin iraki ta kawo wa kasar mu hari, an yi bahasi daban-daban kan hakan sannan kuma an fadi abubuwa masu yawa...to sai dai ko shakka babu wani bangare na manufar wannan wuce gona da iri tana da alaka da manufofin ma'abota girman kai na duniya wadanda kasar Iraki ta yi tarayya da ma'abota girman kan duniya a wannan fagen wanda shi ne fada da juyin juya halin Musulunci, hana bayyanar nasara da kuma tasirin tsarin Musulunci, kashe wa kungiyoyin da suke gwagwarmayarsu ta hanya daga taken riko da Musulunci, kai a takaice dai kifar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran". Jagoran ya ci gaba da cewa: "Ko shakka babu a lokacin da muke magana kan kifar da tsarin Jamhuriyar Musulunci da kuma kawar da juyin juya halin Musulunci, a dabi'ance wannan manufar tana da wani amfanin da za ta samar wa ma'abota girman kan da kuma tabbatar musu da manufofinsu a yankin, wato lamarin da ya shafi man fetur da kuma lamunce musu shi. (yana da kyau kuma a san cewa) wasu dalilai da manufofin suna komawa ne ga ita kanta gwamnatin Iraki (da ta kaddamar da yakin) duk kuwa da cewa a wani bangare su kansu lamurra ne da za su amfani su kansu ma'abota girman kan. A matsayin misali kasar Iraki tana ganin idan hart a sami iko a kan kasar Iran ko kuma alal akalla raba wani yanki na kasar Iran da 'yan'uwansa za su sami iko kan gagaruman albarkatun kasa da ke yankin ko kuma idan ta cimma nasara za ta zama jagorar kasashen larabawa wanda hakan zai ba shi damar iko fadi a ji a yankin Tekun fasha". To wannan kadan kenan daga cikin abubuwan da ya zo daga bakin Jagoran dangane da dalilan wannan yakin wanda ya ke nuni da cewa babbar manufar yakin dai ita ce kifar da gwamnatin Musulunci na kasar Iran wanda bayyanarta ta zamanto barazana ga munanan manufofin ma'abota girman kai na duniya. Daga wadannan bayanai na masana da kuma na Jgaoran juyin juya halin Musulunci za mu iya fahimtar cewa babbar manufar kaddamar da wannan yaki da gwamnatin Saddam Husain ta yi a kan Iran ita ce kawar da gwamnatin Musulunci da kuma juyin juya halin Musulunci da ya sami nasara a kasar. To sai dai kuma a dabi'ance dan'adam ya kan yi kokarin fakewa da wasu abubuwan wajen aiwatar da wani abin da ya ke son aiwatarwa, don haka babu kawo da juna cikin maganar da wasu suke yi na cewa kabilanci, ko man fetur da sauransu su ne ummul aba'isin din yakin. Na'am kasar Iraki tana iya fakewa da wadannan abubuwa wajen kaddamar da yaki a kan Iran, to amma dai babban abin da ya ke a fili shi ne cewa babbar manufarta ita ce kifar da jaririyar gwamnatin Musulunci ta kasar ta Iran, kuma cikin ikon Allah da tsayin dakan al'ummar kasar Iran karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini sun gaza wajen cimma wannan manufar. --------------------------------- Odita Janar Muhammadu Gande wannan shi ne abin da muka tanadar maka dangane da tambayarka kan dalilin wannan yaki gwamnatin Saddam ta kallafawa Iran. Da fatan ka gamsu. Masu saurare a nan ne kuma za mu dasa aya sai kuma a shiri na gaba. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

Tags