Oct 22, 2017 08:10 UTC

Suratur Rum, Aya ta 35-38 (Kashi na 737)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 35 a cikin suratul Rum:

 

أَمْ أَنزَلْنَا عَلَيْهِمْ سُلْطَانًا فَهُوَ يَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُوا بِهِ يُشْرِكُونَ

 

35-Ko kuwa mun saukar musu da wani littafi ne wanda shi ne yake Magana da abin da suka kasance suna shirka da shi.

Wannan ayar ci gaban ayar da ta gab ace ta ne da ke bahasi kan rusa shirka da akidar mushrikai da cewa; Shin mushrikai  da ke yin shirka da allah  suna da wata hujja ko dalili  kan wannan aiki da suke aikatawa? Shin a tsari da rayuwa ta dabia sun ga wata alama  da ke nuni da Allah yanada abokin tarayya ? Ko wani littafi da Allah ya sabko  a gare su  da a cikin littafi ake raya cewa Allah yana da abokin tarayya? To amsoshin wadannan tambayoyi a fili yake babu daya daga ciki da Mushrikai ke dogaro da shi sai dai jahilci da ta'assubanci  da son rai  kuma wannan akida tasu ta bata  babu wani dalili na hankali ko na wahayi da suka dogara shi.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka: Musulunci addini ne na hankali da hujjoji hatta ga masu adawa da shi yana bas u damar kawo dalili da hujjar aiki da suke aikatawa saanin musulunci.

Na biyu: Sabanin tauhidi da ke da hujjoji masu karfi da zurfi ,ita shirk aba ta da tushe balantana dalili ko hujja ta hankali.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 36 a cikin wannan sura ta Rum:

 

وَإِذَا أَذَقْنَا النَّاسَ رَحْمَةً فَرِحُوا بِهَا وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ إِذَا هُمْ يَقْنَطُونَ

 

36- Idan kuma Muka dandana wa mutane rahama sai su yi farin ciki da ita ,idan kuwa wata masifa ta same su saboda abin da hannayensu suka gabatar sai ka gan su suna debe kauna.

Kamar sauran ayoyin da suka gabata wannan ayar ma na bayani kan wani lamari da siffa da mushrikai ko wadanda suka yi hannun rika da imani suka kebanta da ita cewa gas u da girman kai da kuma Ya'asi kamar yadda suke nuna girman kai wajen godewa ni'imomin Allah  haka idan suka fuskanci matsaloli a rayuwa sai ka same su masu ya'asi da fidda kauna .Sabanin mumunai ma'abuta imani na gaskiya masu yin godiya da hakuri a kullum  idan ni'ima ta same su sais u godewa Allah da yayi masu wadannan ni'imomi idan kuwa wata matsala ta tunkare su sai ka same su masu hakuri da juriya ba kasawa.  Abin lura a cikin wannan ayar da sauran ayoyi makamantanta .Ni'ima ramaha ce daga Allah  amma sabaninta kamar ala'I da matsaloli  sun samo asali ne daga ayyukan da muka aikata saboda Allah babu wani abu face lutifi da rahama ga bayunsa ke so amma matsaloli tushensu daga mune mutane da ayyukan da muke aikatawa da bas u dace ba domin Allah bay a zalunci kan bayunsa.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Mutane da bas u yi imani ba ko suke da rauni a imani bas u da juriya kan wata matsala ko bala'ii amma a lokaci guda masu girman kai ne ga ni'imar Allah  da nuna kasawa a rayuwa.

Na biyu: Ni'imomin wannan duniya bas u dawwama don haka kar mutum ya sarkafa da su ko damuwa idan sun kubuce masa ko  nuna kasawa da hakuri.

**************************MUSIC*****************

To daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 37 da 38 a cikin wannan sura ta Rum:

 

أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّ اللَّهَ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاء وَيَقْدِرُ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

 

37- Yanzu ba su gani ba cewa Allah yana shimfida arziki ga wanda ya so yana kuma kuntatawa ga wanda ya so? Hakika a game da wannan lallai akwai ayoyi ga mutanen da suke ba da gaskiya.

 

فَآتِ ذَا الْقُرْبَى حَقَّهُ وَالْمِسْكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ ذَلِكَ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يُرِيدُونَ وَجْهَ اللَّهِ وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
 

38-Sannan ka bai wad an uwa makusanci hakkinsa da miskini da matafiyi. Wannan shi ya fi alhairi ga wadanda suke neman yardarm Allah,kuma wadannan su ne marabauta.

Wannan ci gaban ayoyin da ke bayanin kan wasu mutane maras imani ko karamcin imani  wadanda da zarar sun sami ni'ima sai girman kai da jiji da kai ya mamaye su amma kuma da zarar wannan ni'ima daga Allah ta kubce masu sais u fada cikin yanayi na yanke kauna  to wannan ayoyin da muka saurara na cewa;  mutane wadanda suka yi imani da allah suna da imanin arziki da wadata suna hannun Allah ne  kuma yawa ko karamcin arziki yana rabawa ne cikin ilimi da hikimarsa madaukakin sarki.  Wasu mutane za su tashi tukuru babu dare babu rana wajen neman arziki amma abin da za su samu bai taka kara ya karya ba ,amma wasu kuma suna kokari ne daidai wadaita amma sai Allah ya arzuta su arziki mai yawan gaske. Don haka mu kasance masu kokari daidai gwalgwado  daidai da hankali da yin dogaro da Allah kan samu ko rashinsa. Idan muka yi iyakacin kokarinmu wajen neman arziki amma muka kasa samu kar mu nuna kasawa da fidda kauna  domin duk lokacin da Allah ya gay a dace da mu sami wannan arziki za mu samu da ganin sakamako na alheri kuma mu kasance masu godiya da dogaro da abin da muka samu. Ci gaban ayar na nuni da nauyin mutane kan sauran yan uwansu da cewa: duk wanda Allah y aba shi arziki mai yawa to nauyin da ya rataya kansa ya karu bayan iyalansa da yan uwansa dole kuma yayi tunanin bukatun sauran jama'a da ke rayuwa da shi  kuma da ciyar da mutane amma karkashin neman yardarm allah  ba neman daukaka da sunansa ya fito ba a tsakanin mutane kuma duk abin da aka yi shi ba don Allah ba to karshensa rushewa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyar kamar haka:

Na farko:Idan sun san cewa arziki daga allah ne to bai kamata ba mu yi kasa a guiwa wajen ciyar da mabukata saboda Allah a tsakanin jama'a

Na biyu: idan ciyarwa ba don allah ne ba to wanda ya karba ne zai amfana ba wanda ya bayar ba.

Na uku: makusanta mabukata suna da hakki da hakkoki kan mutum  da ya dace a buya masu daidai gwalgwado.

Na hudu:masu arziki bayan fitar da khumusi da zakka dole kuma su lura da bukatu da halin da matalauta ke ciki a cikin jama'a  da ciyar da su daga dukiyar da Allah yah ore masu ba wai su takaita da abin da ya jawaba a kansu na zakka da khumusi.

Na biyar:addinin musulunci yana bada muhimmanci na musamman kan mabukata domin kawar da talauci a tsakanin jama'a da wannan ke nuni da girma da daukakar addinin musulunci.  

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags

Ra'ayi