Oct 22, 2017 16:32 UTC

Suratu Luqman, Aya ta 17-19 (Kashi na 747)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 17 a cikin wannan sura ta Lukman:

 

يَا بُنَيَّ أَقِمِ الصَّلاةَ وَأْمُرْ بِالْمَعْرُوفِ وَانْهَ عَنِ الْمُنكَرِ وَاصْبِرْ عَلَى مَا أَصَابَكَ إِنَّ ذَلِكَ مِنْ عَزْمِ الأُمُورِ
 

17-Ya kai dana, ka tsai da salla, kuma ka yi umarni da aikata alheri, ka kuma yi hani daga mumunan aiki, kuma ka yi hakuri bisa duk abinda ya same ka, hakika wadannan suna daga manyan al'amura.

A shirye-shiryen da suka gabata mun yi ishara game da wasu nasihohin Lukmana ga dansa, bayan tabbaci da kuma ta'akidi ga abubuwan da suka shafi akida, a cikin wannan aya, Lukuman ya tabo batutuwan da suka shafi ibada da zamantakewa yana mai cewa: bayan amincewa da tauhidi, farko abinda ya rataya kanka shi ne bautar Ubangijin halittu da kuma komawa zuwa gare shi, da hakan ke tabbatuwa , sau da dama a tsai da salla, ka kasance mai tsai da salla, kuma ka karfafa imaninka da ubangijinka a zuciya. Ko da yake salla ita kadai ba ta isa ba, kamar yadda tunani a kan kai shi kadai ba zai wadatar ba, ya kamata, ka kira wasunka wajen aikata ayyukan alheri da sauran kyawawen ayyuka, domin alheri da kuma kyawawan ayyuka su wanzu a tsakanin al'umma, kamar kuma yadda ya zamanto wajibi ya yaki munanan ayyuka, kuma kada ka bari mummuna ya wanzu a cikin al'umma.

A dabi'ance kasancewa cikin al'umma, a kwai bukatar kokari wajen watsa ababe masu kyau da kuma hani a abubuwa munana, da kuma hakan na tare da wahalhalu gami da matsaloli daban daban,saboda masu aikata sabo da munanan ayyuka za su iya nasu kokari wajen nuna adawa da gaskiya, amma mumini bai kamata yayi kasa a gwiwa wajen tunkarar wannan matsaloli, ya zama wajibi ya kasance mai juriya wajen fuskantar wadannan matsaloli, kuma ya tsaya kyam da kafufawansa a hanyar gaskiya  domin kokarinsa ya cimma gaci.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe uku kamar haka:

1-Azama da niya mai karfi wajen cimma  hanyar ubangiji, na daga cikin ababen dake tafiya tare Imani, ba tare da wannan ba, babu wani aiki da zai kai ga kyakkyawan sakamako.

2-Yiwa Yara nasiha game da salla tare da binciken yadda suke tsai da salla, yauni da ya rataya a kan ma'aifa.

3-ya kamata mu bawa yaranmu tarbiya ta yadda za su nauki nauyin shugabanci game da ababen da suka shafi al'umma da zamantakewa, kada su kasance wadanda bas u damu ba game da munanan ayyuka  a cikin zamantakewar al'umma.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya  ta 18 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

وَلا تُصَعِّرْ خَدَّكَ لِلنَّاسِ وَلا تَمْشِ فِي الأَرْضِ مَرَحًا إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَالٍ فَخُورٍ
 

 

18-Kada kuma ka dauke fuskarka daga mutane, kuma kada ka yi tafiya a bayan kasa kana mai takama.Hakika Allah ba Ya son duk wani mai takama mai fariya.

A cikin wannan aya, lukman yayi ishara da wasu munanan dabi'u, sannan kuma ya yi hani da aikata su ga dansa, jiji da kai, dagawa da girman kai, sakamako ne da muguwar tarbiya, a cikin wannan aya an yi ishara da misali na wannan muguwar dabi'a da misalai guda biyu:

Na farko, rashin damuwa da wasu da nufin kaskantar da su, ma'ana wasu mutane saboda suna da suka yi ko shuhura, dukiya ko milki, za su zarabtu da wannan mumunar dabi'a, suna ganin cewa sun fi mutane.

Na biyu: abu na biyu da Lukuman yayi ishara da shi yanayin tafiya a tsakanin al'umma, wasu mutane a maimakon tawaru'I da Kankan da kai, sai su kasance suna tafiya cikin dagawa da girman kai, kamar shugabanin mutane, kuma a ganinsu ya zama wajibi ga kowa ya kaskantar da kai , ya kuma rusana musu.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe biyu kamar haka:

1-kyakkyawar mu'amala da mutane na daga cikin nasihohin Lukuman mai hikima ga dansa, ambato wadannan nasihohi na hikima da ubangiji yayi a cikin alkur'ani mai girma, a hakikanin gaskiya, nasiha ce ga dukkanin al'umma baki daya.

2-wajibi ga iyaye a lokacin da 'ya'yansu suka fara girma, su tarbiyantar da su ta yadda za su amintu daga nau'in cututuka na dabi'u daga cikin su akwai girman kai da dagawa.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya  ta 19 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

وَاقْصِدْ فِي مَشْيِكَ وَاغْضُضْ مِن صَوْتِكَ إِنَّ أَنكَرَ الأَصْوَاتِ لَصَوْتُ الْحَمِيرِ

 

19-Kuma ka tsagaita game da tafiyarka, kuma ka yi kasa-kasa da muryarka, hakika mafi munin muryoyi it ace muryar jakuna.

A cikin ayar da ta gabata, Lukman ya hana dansa munanan ayyuka da dabi'u guda biyu, a cikin wannan aya kuma Lukuman ya kira dansa da aikata wasu kyawawen dabi'u da ayyuka guda biyu,yana mai cewa a tsarin rayukarka ka kiyaye adalci da daidaito. Da hakan zai sanya ga rayu  ba tare da ka jarabtu da ayyuka na fice gona da iri ba, ma'ana kada ka kasance mai fice gona da iri a rayuka, kuma za zamanto wanda bai damu da komai a rayuwarsa ba, saidai ka kasance cikin matsakaiciyar hanya a rayuwa.

Ba wai kawai a mu'amala za ka kasance mai kiyaye daidaito ba, har ma a Magana, kada za zamanto mai Magana kasa kasa ta yadda wasu ba za su ji abinda kake fada ba, kuma kada ka zamanto mai daga murya ta yadda za ka cutar da su, kadda ka yi tsamanin mutane suna jin dadin daga muryarka ba, kuma za su amince da maganarka saboda daga muryar da kake yi, a wajen mutane muryar jakuna, murya ce maras kyau, domin hakka kayi Magana matsakaiciya.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe uku kamar haka:

1-Daga cikin ababen da suka zama wajibi ga iyaye suka koyar da 'ya'yansu, kiyaye yanayin zamantakewa ta hanyar tafiya da kuma Magana.

2-Nisanta daga ayyukan fice gona da iri,daidaito da tsaka-tsakiya a ayyuka, na daga cikin maudu'an da Allah madaukakin sarki yayi wasici da su a cikin alkur'ani mai girma.

3-Iho da daga murya, a wajen Allah abu ne maras kyau, domin haka wajibi ne mu sassauta muryarmu, kuma kadda mu daga muryar da ba ta da amfani.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tags