Oct 22, 2017 16:36 UTC

Suratu Luqman, Aya ta 20-24 (Kashi na 748)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 20 a cikin wannan sura ta Lukman:

 

أَلَمْ تَرَوْا أَنَّ اللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَأَسْبَغَ عَلَيْكُمْ نِعَمَهُ ظَاهِرَةً وَبَاطِنَةً وَمِنَ النَّاسِ مَن يُجَادِلُ فِي اللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَلا هُدًى وَلا كِتَابٍ مُّنِيرٍ
 

20-Yanzu ba kwa gani cewa Allah ya hore muku abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin kassai, Ya kuma cika muku ni'imominsa na sarari da na boye? Daga mutane kuma akwai wadanda suke jayayya game da Allah ba tare da wani sani ba, ba kuma tare da wani littafi mai haskakawa ba.

A cikin shirin da ya gabata, nasihohin Lukuman ga dansa a fagen akida, dabi'u, zamantakewa suka kare, a cikin wannan aya kuwa an dawo kan maudi'in da aka fara kafin wadannan nasihohi da suka shafi sanin Allah, kuma wannan khuduba ce ga dukkanin mutane, ubangiji ya halicci sama da kasa ta yadda ya tsara su su kasance masu hidima ga ku mutane, tsarin dabi'a kamar rana da wata a sama, juyawar kasa ko juyawar kwallon duniya, sharadi ne dake tsaya rayuwar mutane, ruwa da taiku, nau'in ma'adinai na karkashin kasa da na samanta, nau'in dabbobi na doron kasa da na cikin ruwa, nau'in itace da tsirai gami da albarkatun noma, dukkanin wadannan ababe an halicce su ne domin mutane, wasu daga cikinsu kai tsaye suna karkashin kulawar mutane, wasu kuma cikin ikon ubangiji, amfaninsa na isa zuwa ga mutane. Kari ga wadannan ni'imomi na zahiri dake biyan bukatun jikin mutum, Ubangiji ya aiko ma'aika da annabawa tare da litattafai, wadanda suke magance bukatun tunani da na ruhin dan adam, da kuma suke yin sanadiyar daukaka da kamalar mutum, amma duk da wannan ni'ima da Allah madaukakin sarki ya horewa bayinsa, a cikin tsahon tarihi, maimakon su yi godiya game d wadannan ni'imomi, sai dai zalinci, jayayya ba tare da wani dalili na hankali ba.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-Mutum tauraro ne a tsakanin halittu, sama da kasa da abinda ke cikinsu an halicce su ne domin hidima ga mutane.

2-Ni'imomin ubangiji ga dan adam, masu yawa ne kuma nau'I daban daban ne, na zahiri ne ko na badini, domin haka menene ya sanya Mutum ba ya godewa Ubangijinsa?

3-Bahasi, jidali da jayayya zai kasance mai amfani, idan ya kasance bisa tushen ilimi da hankalin dana dam ko kuma shiriya da littafin Ubangiji.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya  ta 21 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا مَا أَنزَلَ اللَّهُ قَالُوا بَلْ نَتَّبِعُ مَا وَجَدْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا أَوَلَوْ كَانَ الشَّيْطَانُ يَدْعُوهُمْ إِلَى عَذَابِ السَّعِيرِ
 

 

21-Idan kuma aka ce da su"Ku bi abin da Allah ya saukar" sai su ce A'a, mu muna bin abin da muka sami iyayenmu ne a kansa" Yanzu (sa yi haka) ko da shaidan ya zamanto yana kiran su zuwa ga azaba ta (wutar) sa'ira?

A cikin ayar da ta gabata mun bayyana cewa wadancan  sun kasance masu shakku game da Ubangiji, ba tare da wani dalili bayannani ba, wannan aya kuwa na cewa dalilin da dama daga cikin su shi ne kiyaye al'adu na magabatansu da kuma biyayya ga mutanen da suka gaba ce su, wadannan mutane ba a shirye suke ba su bar addinin magabatansu ba,  a maimakon su goyi bayan shiriyar Ubangiji, sai suka bi bayan abubuwan karya da iyayensu suka kasance a kai, a yayin da hakan tunani maras kyau, kuma na shaidani da zai yi sanadiyar su ma wannan gungu su kasance kamar magabatansu , su shiga cikin wuta.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-Bangaranci na addini a kan akida maras kyau da magabata suka yi Imani da shi, biyayya ido rufe, na daga cikin ababen da suke hana karbar gaskiya, da kuma suke hana hankali da tunanin mutum fahimtar gaskiya.

2-kiyaye kayan tarihi da al'adun al'umma, na da kima matukar bai yi karo da hankali da addini ba, idan kuma ba haka bay a kan iya zama sanadiyar faduwar al'umma.

3- ko wani lokaci kuma cikin ko wani yanayi ,Shaidani na kiran mutum zuwa ga muguwar hanya.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na  22 zuwa 24 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

وَمَن يُسْلِمْ وَجْهَهُ إِلَى اللَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى وَإِلَى اللَّهِ عَاقِبَةُ الأُمُورِ
 

 

22-Wanda duk kuwa ya mika kansa ga Allah, yana kuma mai kyautatawa, to hakika ya yi riko da igiya kwakkwara, kuma karshen al'amura zuwa ga Allah ne.

 

وَمَن كَفَرَ فَلا يَحْزُنكَ كُفْرُهُ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ فَنُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
 

23-Duk kuwa wanda ya kafirta, to kada kafircinsa ya bata maka rai. Zuwa gare Mu ne kawai makomarsu take, sannan Mu ba su labarin abin da suka aikata. Hakika Allah masanin asirin zukata ne.

 

نُمَتِّعُهُمْ قَلِيلا ثُمَّ نَضْطَرُّهُمْ إِلَى عَذَابٍ غَلِيظٍ

 

24- Za mu jiyar da su dadi dan kadan sannan mu tilasta su zuwa ga azaba mai kauri.

Wadanna ayoyi , dangane da da'awar ubangiji sun kasa mutane zuwa kashi biyu: kashi na farko sun karkata zuwa ga ubangiji gaba dayansu, kuma sun meka wuya  tare da sallamawa zuwa gareshi, kashi na biyu kuwa sun zabi hanyar jayayya da zuja baya game da kiran Ubangiji, lamarin da ya kai su kafircewa ga Allah madaukakin sarki.

Kashi na farko sun yi riko da igiya kwakkwara ta shiriya ubangiji, kuma sun bi hanya ta gaskiya, kuma su ne masu aikata alheri da kuma kyautatawa zuwa ga wasunsu, kuma kyakkyawan sakamakon na jiransu. Su kuma kashi na biyu ko da sun amfanu da duniya da kuma dadinta to a karshe za su samu mumunan sakamako, kuma a Duniya da Lahira za su fuskanci damuwa da wahalhalu nau'I daban daban, a Duniya nau'I daban, haka zalika a lahira ma wani irin nau'I ne na daban.

Duk da cewa kafirai suna cutar da Annabin Rahama (s.a.w.a), kuma ba za su ji dadi ba, domin za su fuskanci azabar su, to saidai Ma'aiki (s.a.w.a) ya kasance mai damuwa game da halin da za su shiga na kaucewa hanya, amma hakan ba shi da wata fa'ida saboda sun zabi hanyar bata da kansu, kuma Manzo (s.a.w.a) ba zai iya tilasta musu yin Imani ba.

Daga cikin wannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-idan dukkanin halittu na duniya sun meka kansu ga umarnin Ubangiji, kuma Allah ta'ala ya sanya su su kasance karkashin ikon mutum, to me ya sanya mu mutane ba mu meka wuya ga Ubangiji 

2- domin kare matsayarsa, mutun a duniya yana zaben abinda zai yi garkuwa da shi, ko yayi garkuwa da wasu Mutane, ko kuma yayi da wani abu, shi kuma mumini da Allah madaukakin sarki kawai yake garkuwa kuma a wajen sa yake neman mafuka, domin su muminai suna riko da igiya kwakkawara ta Ubangiji, kuma su yi aiki na gari, da hakan zai sanya su cimma hanyar tsira, a cikin wasu riwayoyi an bayyana cewa Manzon Allah (s.a.w.a) da shugabanin shiriya 12 na iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka su ma igiyar ubangiji ne kwakkwara.

3-A rayuwar Duniya, mu zabi hanyar da za mu bi bisa hangen abinda zai so nan gaba da kuma yin tunani, domin karshen rayuwa mu faskanci mumunan sakamako da azabar Ubangiji.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags