Oct 22, 2017 16:42 UTC

Suratu Luqman, Aya ta 25-28 (Kashi na 749)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 25 da na 26 a cikin wannan sura ta Lukman:

 

وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لا يَعْلَمُونَ
 

25-Wallahi kuma in da za ka tambaye su:"wane ne ya halicci sammai da kassai? Lallai za su ce:"Allah ne"(to) ka ce:"Alhamdu lillahi".A'a, yawaicinsu dai ba sa sanin (haka).

 

لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ
 

26-Abin da yake cikin sammai da kassai na Allah ne, Hakika Allah shi ne Mawadaci Abin yabo.

Wadannan ayoyi na ishara game  bayyanannun al'amura da suka samu amincewar dukkanin mutane daga cikin su har mushrikai masu bautar gumakai, suna cewa shin idan z aka tambaye su wane ne ya halicci duniya? Ba tare da wata tattama ba za su ce Allah!saboda da haka dukkanin mutane za su fada cikin tunani a kan cewa shin sub a hallitar Allah ba ne ba? Ko da mushrikai masu bautar gumaka suna cewa gumaka bas u ba ne suka halicci halittu da Duniya, saidai abokanin tarayyar Ubangiji ne wajen tafiyar da al'amura, ci gaban ayar na cewa idan Allah madaukakin sarki shi ne ya halicci Duniya, to  shi ne Ubangiji da kuma mamllakin halittu , kuma shi ne mai hukunci a kan komai, don shi ne abin yabo kuma shi kadai ne ya ceccanci bautawa, ba wasu mutane ko abubuwa na daban ba.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

1-Mushrikai bas a inkari na halittar Ubangiji, saidai  tunshen kaucewarsu daga kan hanya shi ne wajen bautar gumaka da kuma neman waraka daga gare su.

2-Sanin Allah abu ne dake cikin fitirar ko wani dana dam, ko da mushrikai sun yardar da cewa Allah shi mahalicci.

3-mafi yawa daga cikin kaucewa hanya, yana samo asali ne daga rashin sani da jahilci, tayar da Annabawa da ma'aika gami da waliyan Allah, da nufin fadakar da mutane ne tare da sanya su a hanya na kadda su kaucewa hanya su fada cikin bata.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya  ta 27 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

وَلَوْ أَنَّمَا فِي الأَرْضِ مِن شَجَرَةٍ أَقْلامٌ وَالْبَحْرُ يَمُدُّهُ مِن بَعْدِهِ سَبْعَةُ أَبْحُرٍ مَّا نَفِدَتْ كَلِمَاتُ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
 

 

27-Idan kuwa da a ce , abin da yake ban kasa na bishiyoyi alkaluma ne, kogi kuma ya zama tawadarsu, bayansa kuma akwai wasu koguna guda bakwai (a rika rubuta ayoyin Allah da su, to da kalmomin na Allah ba za su kare ba. Hakika Allah mabuwayi ne Mai Hikima.

Wannan aya tana ishara ne game da girmar halittu tana mai cewa ilimin dan adam game da hallitu kwarai ma takaicecce ne, domin idan maliya za ta koma tawadda shi kuma itacen duniya za su zamanto abin rubutu da ba za su iya rubuta halittun ubangiji ba.

A cikin Duniyar mutum, kalmomi su ne masu bayyana manufa, amma abinda ake nufi da kalmomi a cikin wannan aya shi ne nau'o'I halittun ubangiji a cikin wannan duniya da dukkanin su suke bayyana ilimi da karfin maras karshe na mahalicci, yawaicin lokaci masana da masu ilimi suna amfani da alkalami gami da takarda wajen rubuta abubuwan da suke son bayyanawa da kuma bayyana iliminsu, to amma ilimin ubangiji ba shi da iyaka, ko da kuwa dukkanin ruwan da ake shin a Duniya zai zamanto tawadda da kuma itacen da ake dasu na Duniya su zamanto alkalami ba za su iya rubuta ilimin Allab ba, haka kuma ba za su iya rubuta halintun Allah ba, tausayinda da ni'imominsa da ba su da karshe, ba za su iya rubutawa ba.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

1-Allah girman ya fice ace zuwa yanzu mutum ya fahimci halittunsa, Duniya kadda mu yi mata karamin hange da iyakancewa, wanda hakan zai sanya mu fada cikin karamin tunani.

2-Dukkanin halittun Ubangiji suna shai da ne ga mahalicci guda daya, domin haka mu kiyaye da neman wasu abin bauta da aka kirkiro, saboda ilimi, buyawa, hikima dukkaninsu daga ubangijin duniya daya ne.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya  ta 28 a cikin wannan sura ta Lukuman:

 

مَّا خَلْقُكُمْ وَلا بَعْثُكُمْ إِلاَّ كَنَفْسٍ وَاحِدَةٍ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ
 

28-Halitta ku da tayar da ku bai wuce tamkar na rai daya ba.Hakika Allah mai ji ne mai gani.

A ci gaban ayar da ta gabata wacce tayi bayyani game girman halittun ubangiji, wannan aya kuwa tana ishara ne game da kudira da karfin da bas hi da karshe na ubangiji, yana mai cewa idan Allah madaukakin sarki yana son kashe mutane gaba daya na tsahon tarihi, lokaci daya ya kuma tayar da su ranar alkiyama lokaci daya, aiki ne mai sauki a gare shi, a mahangar ilimi da karfi masu iyaka namu suke ganin cewa yawa na haifar da matsala, amma a wajen ubangiji babu babbanci tsakanin yawa da kadan, komai a wajen sa mai sauki ne.

Ci gaban ayar na cewa saboda shi Ubangiji mai ji mai gani ne game da dukkanin ayyukan bayinsa kuma ya nada ilimi da masaniya a kan ayyukan su, bisa wannan tushe ne zai sakawa wadanda suka yi aiki mai kyau da lada, sannan yayi azaba ga wadanda suke yi ayyuka munana.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

1-Lokaci, wuri da yawa ya nada ma'ana a wajen dana dam, amma a ilimi da kuma kudurar ubangiji, yawa wata halitta ce, haka zalika sarrafa zamani da lokaci bas hi da wani tasiri, misali a wajen halittar mutum daya da mutane biliyan daya babu babbanci, komai a wajensa mai sauki ne.

2-idan mun san cewa dukkanin maganganunmu Allah madaukakin sarki yana ji da kuma dukkanin ayyukanmu yana gani, za mu taka tsatsan, kuma ba za mu kaucewa hanya diyawa ba.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

 

 

 

 

Tags