Dec 06, 2017 09:27 UTC

Suratus Sajdah, Aya ta 20-25 (Kashi na 755)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 20 da na 21 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

وَأَمَّا الَّذِينَ فَسَقُوا فَمَأْوَاهُمُ النَّارُ ۖ كُلَّمَا أَرَادُوا أَن يَخْرُجُوا مِنْهَا أُعِيدُوا فِيهَا وَقِيلَ لَهُمْ ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ
 

20-Amma kuma wadanda suka kafirce, to makomarsu wuta ce, ko da yaushe suka yi niyar fitowa daga gare ta sai a mayar da su a cikinta a kuma ce da su:" ku dandani azabar wuta  wadda kuka kasance kuna karyata ta."

 

وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنَ الْعَذَابِ الْأَدْنَىٰ دُونَ الْعَذَابِ الْأَكْبَرِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ

 

21-Wallahi kuma tabbas za Mu dandana masu (wani abu) daga azabar da ta fi kankanta(ta Duniya) kafin azabar da ta fi girma(ta Lahira) don su dawo (daga bata).

A shirin da ya gabata, Ubangiji ya bayyana cewa mumini da kafiri a wajensa ba guda ba ne, muminai saboda ayyukan da suka yi sun caccanci shiga aljanna, kuma a ciki suna da matsayi mababbanta, wadannan ayoyi kuwa na cewa amma mutanen da suke da'awar Imani kuma a aikace ba sa bin umarnin Ubangiji, kuma suna bijewa umarnin sa, za su fuskanci azabar wuta, kuma ba su da wani zabi face wannan.

Ko da yake a nan duniya, ta hanyoyi daban daban an yi ta yi musu horo, a kan mai yiyuwa za su tuba, to amma ba su bar munanan ayyukansu ba, za su fuskanci azaba ranar Lahira, domin a kiyama an rufe hanyar karbar tuba, kuma babu damar komowa Duniya.

Bisa wasu hadisai da aka ruwaito, wasu daga cikin bala'o'I, rashin lafiya da wahalhalu da mutum ke fuskanta a nan Duniya nau'I ne na horon Ubangiji domin tunatar da mutum ya tuba, ya gyara ayyukansa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Fasikanci da sabo , wani lokaci su kan mamaye mutum, kamar ka ce bai yarda da ranar Kiyama ba ko kuma munkiri na tashin alkiyama.

2-Azabar Ubangiji, ba ta kebbanta da ranar lahira ba, a wannan duniya ma, Ubangiji yana azabtar da mutane, kuma wannan wata ni'ima ce domin ya horar da su kan su tuba su gyara ayyukansu tun a nan duniya.

3-fishin ubangiji a nan duniya na a matsayin tarbiyar da mutane su hadu da rahamar Ubangiji.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi ta 22 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ ثُمَّ أَعْرَضَ عَنْهَا ۚ إِنَّا مِنَ الْمُجْرِمِينَ مُنتَقِمُونَ

 

22-Babu wanda ya fi zalinci fiye da wanda aka yi wa wa'azi da ayoyin Ubanigijinsa sannan ya bijire musu.Hakika Mu masu sakawa kafirai ne.

A cikin wannan aya Allah madaukakin sarki ya kira wadanda suka san gaskiya daga ayoyin alkur'ani mai tsarki da kuma umarnin Ubangiji suka kuma juya mata baya da azzalimai wadanda suka caccanci azabar Ubanigiji.a dabi'ar kur'ani, duk wanda ya zalinci kansa har ya fada cikin kafirci, ana kiransa da azzalimi, to ina ga wadanda suke zalintar wasunsu.Mutum mumini har abada ba ya zalintar dan uwansa ko kuma wasu, amma wanda ya fiahimci gaskiya ya rufe ta, ya kuma zafi hanyar kafirci, cikin sauki zai iya rufe ido a hakkokin mutane ya kuma zalince su.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Taurin kai da jayayya, na sanda mai so lokacin da aka tunatar da shi, mai makon ya bar abinda yake yin a sabo, sai ya ci gaba a kan laifin da yake yin a sabo.

2-mu'amala da mushrikai, wata rana bayan tunatarwa, akwai bukatar horo da tsanantawa a gare su.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi daga na 23 zuwa na 24 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ فَلَا تَكُن فِي مِرْيَةٍ مِّن لِّقَائِهِ ۖ وَجَعَلْنَاهُ هُدًى لِّبَنِي إِسْرَائِيلَ

 

23-Hakika kuma Mun bai wa Musa littafi,to kada ka kasance (kai Manzo) cikin kokwanto na saduwa da shi, Muka kuma sanya shi shiriya ga Bani-isra'ila.

 

وَجَعَلْنَا مِنْهُمْ أَئِمَّةً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا لَمَّا صَبَرُوا ۖ وَكَانُوا بِآيَاتِنَا يُوقِنُونَ

 

24-Muka kuma sanya Shugabanni daga cikinsu masu shiryarwa da umarninmu don su yi hakuri, sun kuma kasance suna sakankancewa da ayoyinmu.

 

إِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

 

25-Hakika Ubangijinka Shi ne zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alkiyama game da abin da suka kasance suna sassabawa a kansa.

Da farko wadannan ayoyi suna ishara ne game da aiko annabawa tare da litattafan Allah masu tsarki a tsahon tarihi, Allah madaukakin sarki ya ce: ba wani kokwanto mune muka ba Musa Littafi domin ya shiryar da Bani-isra'ila, ya kubutar da su kuma daga kangin bakin milki na fir'auna, a tsakanin wannan al'umma, wasu sun kasance a tare da Musa, suka yi hakuri a yakin zalincin da ya yi da fir'auna, wadanda mutane da suke tsayin daka da juriya tare fir'auna su ne suka samu tabbaci da yakini game da alkawarukan Ubangiji da Attaura, suka kuma iya galaba a kan makiya tare da cimma shugabancin al'umma, bisa dalilai na Littafin Allah da umarnin ma'aikin Allah wadannan mutane sun jagoranci al'umma tare da zartar da hukuncin Allah a doron kasa.

Wadannan su ne muminai na gaskiya, da suka kasance cikin inuwar Imani da juriya har suka cimma jagorancin al'umma, domin su ba su kasnce masu bin ra'ayi ko son zuciyarsu da na mutane ba, saidai sun kasance masu biyayya ga umarnin ubangiji, kuma dukkanin ayyukansu sun kasance bisa tsari da kuma dokokin Ubangiji.wadannan sun kasance masu gabatar da hukuncin Ubangiji a kan ra'ayinsu, kuma a maimakon bin son zukatansu, bisa tushen littafin Allah da dokokin Ubangiji suke yin hukunci.

Ko da yake al'ummar bani-isra'ila sun fuskanci sababi a tsakanin su wanda hakan yayi sanadiyar rarrabuwar kwunansu, sanadin wannan sabanin kuma shi ne nisanta daga gaskiya tare da bin son rai, domin haka ne cikin kakkausar lafazi, Allah madaukakin sarki ke cewa: wannan gungu na mutane da suka yi sanadiyar rarrabuwar kawunan al'umma, su san cewa hisabinsu na wajen ubangiji, a ranar tashin alkiyama, kuma bisa asasi da tushen adalci na ubangiji za a hukunta su.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku  kamar haka:

1-aiko da annabawa, wani abu ne dake faruwa a tsahon tarihi, domin hakan kafin tayar da ma'aikin musulinci, an aiko da annabawa masu yawa, kuma bai kamata ba game Annabawa ko ma'aikan da aka tayar, a sanya shakku ko kokwanto game da annabawan da aka tayar kafin ma'aiki(s.a.w.a).

2-Imani, tabbaci da juriya a hanyar Allah, na daga cikin sharudan da suka zama wajibi ga ko wani shugaba, domin haka ya zama wajibi ga mutum domin cimma manufa, ya kasance mai tabbaci, kuma har zuwa matsayi ya kasance mai juriya har ya samu sharudan da suka dace na shugabantar Al'umma.

3- bai kamata zuciyar shugaban addini ta karaya ba a ayyukansa na shiryar da al'umma, saboda ko wani lokaci akwai sabani.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

Tags