Jan 25, 2018 17:00 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata mun kawo muku wato aya ta 59 da kuma ta 83 cikin suratu nisa'I wadanda suka bayyani game da tambayar da muka bujuro da ita na mahimancin fuskokocin bukatuwa zuwa ga Imami ko shugaba ma'asumi cikin ko wani zamani bayan fakuwar ma'aikin Allah (s.a.w.a) har zuwa ranar alkiyama, wadannan ayoyi guda biyu masu albarka sun bayyana mana cewa daga tausayi da lutufin Allah madaukakin sarki ga bayinsa ya sanya musu shugaba ko Imami ma'asumi daga cikin majibinta al'amuransa ya zamanto makoma garesu na sanin hukunce hukuncen ubangiji da magance sabani yayin da suka samu wani sabani ko jayayya cikin al'amuransu, da wannan ne kuma kai ceto su daga fadawa cikin kangi da bautar shaidan wanda shi a kulun kokari yake ya sanya sabani da rikici a tsakanin mutane domin ya kange su daga bin hanyar Allah madaukakin sarki, kuma wannan shi ne abinda hadisai da dama suka bayyani kansu, za mu zabo muku wasu daga ciki? Amma kafin nan, sai a dakacemu da wannan.

***************************Musuc*****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, shirin na yau zai fara da riwayar da Shekh Saduk ya ruwaito cikin Littafinsa mai suna Ma'anil-Akhbar daga shugaban muminai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya fada mini cewa Hakika Ubangijina madaukakin sarki ya bani labarin cewa Hakika ya amsa mini bukata ta a game da kai Ya Ali da kuma sobayanka da za su kasance bayanka, Ali (a.s) ya ce sai n ace ya ma'aikin Allah su waye sobaye na bayana? Sai ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya cewa  su ne wasiyai daga cikin iyalan gidana da za su tarar da nib akin tabkina, dukkaninsu shiryayyu ne masu shiryarwa, ba ya cutar da su wanda yake kaskantar da su, su suna tare da Alkur'ani kuma Alkur'ani na tare da su, ba ya rabuwa da su, kuma shi ma bay a rabuwa da su, ta hanyar su ne al'umma ta za ta yi nasara, kuma ta hanyarsu ne za a yi musu ruwa, kuma za a yaye musu wani bala'I, kuma ta hanyar su ne ake karba addu'ar bayi.

A bayyane yake masu kasancewarsu tare da alkur'ani mai girma da kasancewar shi alkur'ani mai girma a tare da sub a sa rabuwa shike tabbatar da cewa duk abinda za su fada daga cikin alkur'ani mai girma ne kuma kalaman ubangiji ne da babu kuskure cikinsa, kuma su ne ke magance duk wani sabani da jayayya na tsakanin al'ummar musulmi, ta hanyar su ne al'ummar Annabi Muhamadu (s.a.w.a) za ta yi nasara, kuma ta hanyar su ake kare duk bala'I na jayayya da kuma yiwa shaidani la'ancecce biyayya.a cikin littafin Nahjul-balaga, an ruwaito hadisi daga shugaban muminai Aliyu bn Abi talib (a.s) cikin kalamansa na mayar da martini game da abinda Khawarijawa suka kafa kansa na yin inkari game da hukunci mutane da suke cewa mu ba mu amince da hukuncin mutane ba, kuma hakika abinda zai yi mana hukunci shi ne alkur'ani, hakika shi Alkur'ani rubutu ne daga cikin littafi ba ya Magana, kuma wajibi ne ya kasance mai fassara shi, kuma hakika mutane za su yi Magana a mamadinsa, a yayin da mutane suka kira ayi mana hukunci da alkur'ani mai girma, bai kasance bangaren guda masu biyayya da littafin Allah, alhali Allah madaukakin sarki na cewa:( sannan idan kuka yi sabani game da wani abu, to sai ku mai da shi zuwa ga Allah (watau Alkur'ani) da Manzonsa) sannan Imam (a.s) ya ce:ku mayar da shi zuwa ga Allah  ayi hukunci da littafinsa, ku mayar da shi zuwa Manzonsa, mu dauki sunarsa, idan za a yi hukunci da gaskiya cikin littafin Allah to mune mafi caccanta da mutane da shi Alkur'ani, kuma idan za a yi hukunci da sunar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, to mune mafi caccanta da muka 'ya'yansa da mutane a game da sunarsa).

********************Musuc**************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na karamin sani kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai yi bayyani game da wata riwaya makamanciyar wacce ta gabata da aka ruwaito cikin littafin Al-ihtijaj inda a cikinsa Imam Ali(a.s) yake ishara game da masu tarjamar Littafin Allah da sunar Annabinsa (s.a.w.a), cikin wani dogon hadisi yana fadar cewa:(Kuma hakika Allah ya sanya ilimi ga ahlinsa sannan kuma ya wajabta yi musu biyayya yana fadar cewa:( ku bi Allah kuma ku bi manzo, da kuma mjibintan al'muranku) sannan ya ce:( Da dai  za su komar da shi(watau labarin) zuwa ga Manzo ko kuma majibinta al'amura daga cikinsu, lallai da wadanda suke tace shi (labarin) daga cikinsu sun gane shi) a yayin da wani mutum ya tambaye shi game da ma'anar al'amari na cikin majibintan al'amura, sai Imam (a.s) ya ce (shi al'amari) shi ne abinda mala'ika ke saukarwa cikin ko wani Dare da a cikinsa ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima daga dabi'u, arziki, ajali, aiki, shekaru, rayuwa, mutuwa, da ilimin gaibi na samai da kasai, da kuma mu'uzujojin da babu wanda ya kamata face saboda Allah da kuma zababbunsa da kuma bulaguro tsakaninsa da halitunsa).

A karshen masu saurare,za mu nakalto wata riyawa a cikin Littafin Al-Ihtijaj, fadar shugabanmu Imam, shugaban shahidai babban Abdallah Husain amincin Allah ya tabbata a gare shi cikin wata khudubar da yayi  yana mai cewa:(mu ne rundunar Allah masu galaba,zuriyar ma'aikin Allah (s.a.w.a) makusanta, iyalan gidansa tsarkaka, kuma daya daga cikin nauyayen shiriya, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya sanya mu na biyun littafin Allah tabaraka wa ta'ala da a cikinsa ake rarrabe komai da komai, ya dora yaunin fassarar Alkur'ani a kanmu, domin ta'awinsa ba ya shige mana saidai muna bin hakikaninsa….sannan Imam Husain (a.s) ya ce: ku yi mana da'a da biyayya, domin yi mana biyayya wajibi ne, domin ta kasance tabbatatta da da'ar Allah da ma'aikinsa, Allah madaukakin sarki ya ce: :( ku bi Allah kuma ku bi manzo, da kuma mjibintan al'muranku sannan idan kuka yi sabani game da wani abu, to sai ku mai da shi zuwa ga Allah (watau Alkur'ani) da Manzonsa) suratu nisa'I Aya ta 59 sannan kuma a wata Ayar yana mai cewa:( Da dai  za su komar da shi(watau labarin) zuwa ga Manzo ko kuma majibinta al'amura daga cikinsu, lallai da wadanda suke tace shi (labarin) daga cikinsu sun gane shi (labarin da ya kamata su wasta). Da ba don falalar Allah ba a gare ku, da kuma rahamarsa, da ba shakka kun bi shaidan(kan abinda yake kawata muku na miyagun abubuwa) in ban da 'yan kadan daga cikinku) suratu Nisa'I aya ta 83, sai Imam (a.s) ya ce ina gargadinku da bin hanyoyin shaidain domin shi makiyinku ne mabayyani, da fatan Allah madaukakin sarki yak are mu daga bin hanyar shaidan domin albarkar riko da Alkur'ani mai girma da kuma na ma'aikin Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka.

**************************Musuc******************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.

 

 

 

Ra'ayi