Jan 25, 2018 17:10 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau  ta yaya za muyi kafa dalili da suratul kadari kan cewa kasa ba za ta kasance ba tare da shugaba ko imami ma'asumi ba cikin ko wani zamani har zuwa ranar alkiyama? amma kafin amsa wannan tambaya sai a dakacemu da wannan.

************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, da farko idan muka la'akari za mu ga cewa suratu kadari tana bayyani ne game da saukar Alkur'ani mai girma cikin daren Lailatul-kadari mai albarka, da kuma falalarsa tare da tabbaci na Ambato abubuwa guda biyu masu mahimanci, na farko shi ne Ambato surar da fi'ilin Mari, shi ne saukar alkur'anin(Hakika Mu Muka saukar da shi(alkur'ani ) a cikin daren lailatul kadari) suratu kadari aya ta farko, abu na biyu kuma shi ne Ambato shi cikin sigar fi'ili mudari'I da yake nuni da ci gaba da kuma rashin yankewa Allah madaukakin sarki ya ce(Mala'iku da Ruhu (watau mala'ika jibrilu) suna sauka a cikinta da dukkanin al'amura da izinin ubangijinsu) suratu kadari aya ta 4. Irin wannan mulahaza kuma zamu samu cikin wani wuri na daban da alkur'ani mai girma ya Ambato maganar lailatul-kadari mai albarka, hakika cikin suratu Dukhan Allah madaukakin sarki ya ce:(HA MIM Allah ne ya san abin da yake nufi da wannan*(Allah) Yana rantsuwa da littafi mabayyani (shi ne Alkur'ani).*Hakika Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka. Hakika Mu masu gargadi ne(daga azaba).a cikinta ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima* al'amari ne dagawurinmu,hakika Mu Mun (kasance) Masu aikowa ne (da manzanni).*Wata Rahama ce daga Ubangijinka, hakika shi shi ne Mai ji Masani) suratu Hamin daga aya ta farko zuwa ga aya ta 6, domin haka wannan lamari zai ci gaba cikin ko wani daren lailatul-kadari, ma'ana Mala'iku da Ruhu (watau mala'ika jibrilu) suna sauka a cikinta da dukkanin al'amura da izinin ubangijinsu yayin da a cikinta ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima,hakika ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa daren lailatul kadari zai kasance har zuwa ranar tashin alkiyama, kuma a hakan haka ne al'ummar musulmi na mazhabobi gaba daya suka tayi, duk da cewa akwai sabani a game wannan dare, wasu sun tafi a kan daren 23 na watan ramadana, wasu kuma sun tafi a kan daren 27 na watan ramadana, to saidai tambayar da za ta biyu baya nan shi ne a kan wanene za a saukar da mala'iku gami da mala'ika jibrilu a daren lailatul-kadari cikin ko wata shekara da umarnin ubangiji da kuma tafsilinsa da a cikinsa ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima har zuwa daren lailatul-kadari mai zuwa? Wannan amsawa za mu same ta cikin alkur'ani mai girma kansa.

Masu  saurare, a neman samun amsar tambayar da ta gabata a gare da ayoyin suratul kadari da suratu Dukhan da suke bayyani kan cewa mala'ika da ruhu (mala'ika jibrilu) suna sauka a cikinta da dukkanin al'amura da izinin ubangijinsu yayin da a cikinta ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima, idan muka koma cikin Alkur'ani za mu samu ya sarraha cewa hakika wadanda suke shiryarwa da umarnin Allah su ne wadanda Allah ya sanya su shugabani ga mutane, Allah tabarka wa ta'ala ya ce:(Muka kuma sanya su shuwagabanni masu shiryarwa zuwa ga addininmu,muka kuma yiwo wahayi zuwa gare sun a aikata alheri da tsai da salla da ba da zakka, sun kuwa zamanto masu bauta masa ne) suratu anbiya'I aya ta 73, har ila yau cikin suratu sajadati Allah madaukakin sarki ya ce:(Muka kuma sanya shugabanni daga cikinsu masu shiryarwa da umarninmu don su yi hakuri, sun kuma kasance suna sakankancewa da ayoyinmu) suratu sajadati aya ta 24. Ganin cewa mala'iku da mala'ika jibrilu suna sauka da izinin ubangijinsu da abinda yake rarrabawa al'amarin shiriyarsa na al'amuran halitunsa cikin daren lailatul-kadari daidai kwalkwado a kan wanda Allah ya sanya ko kuma ya zabe shi shugaba ga mutane da zai shiryar da umarninsa madaukakin sarki, ganin cewa daren lailatul-kadari zai dawwama cikin ko wata shekara har zuwa ranar alkiyama, to ya zama wajibi da samuwar shugaba ko imami ma'asumi daga Allah madaukakin sarki da za a dinga yi masa bayyani game da al'amrin halittu da a cikinta ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima na tadbiri na al'amuran bayi.

*****************************Musuc**************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kada a sha'afa shirin na karamin sani kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, wannan hakika da alkur'ani mai tsarki ya bayyana, hadisai da dama sun ta'akidi kansa sannan sun bayyana bayyana misdakinsa, bari mu Ambato wasu daga cikinsu, misali cikin littafin kafi, an ruwaito hadisi daga ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya fadawa sahabansa cewa:(ku yi Imani da daren lailatul-kadari, hakika ta kasance ta Aliyu bn Abi talib da kuma 'ya'yansa sha daya baya na). har ila yau an ruwaito wani hadisi daga Shugaban muminai (a.s) ya fadawa Ibn Abas:( Hakika Daren lailatul Kadari yana sauka  cikin ko wata shekara, kuma hakika a cikin wannan dare, ana saukar da al'amarin shekara, da kuma al'amuran majibinta bayan ma'aikin Allah (s.a.w.a) Ni da sha daya daga cikin 'ya'yana shugabani ne muhadisai), a cikin wani hadisi kuwa da aka ruwaito daga shugabanmu Imam Sajjad Aliyu bn Husain zainul-abidin (a.s) dangane da suratul-kadari, ya ambata cewa fitina ce wadanda suka yi ridda ta hanyar yin inkari da dawwamar daren lailatul-kadari cikin ko wata shekara sannan ya bayyana ilolin inkarinsu da cewa:(domin su idan sun ce lailatul kadari ba ta kushe ba, dole ne ya kasance ga Allah a cikinsa akwai wani al'amari, kuma idan sun tabbatar da wannan al'amari, ba su da wanda sahibin a game da wannan al'amari), ma'ana dole ya zamanto an samar da wani shugaba ma'asumi da za a dinga yi masa bayyani na al'amarin ubangiji cikin ko wani daren lailatul-kadari, yayin da yake bayyani a game da hanyoyin bayyana hujjoji  wajen tabbatar da Imamanci da kuma ci gaban har zuwa ranar tashin alkiyama ga masu inkari shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(Yak u al'ummar shi'a, ku kafa dalili da suratul kadari ku rabauta, na rantse da Allah ita hujjar Allah ce ga a kan bayi bayan ma'aikin Allah (s.a.w.a), kuma hakika ita shugabar Addininku ne ce kuma ita ce abin kira ga iliminmu, Ya ku jama'ar shi'a ka kafa hujja da :(HA MIM Allah ne ya san abin da yake nufi da wannan*(Allah) Yana rantsuwa da littafi mabayyani (shi ne Alkur'ani).*Hakika Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka. Hakika Mu masu gargadi ne(daga azaba) saboda ita na kebebben al'amari ne bayan ma'aikin Allah (s.a.w.a).

**************************Musuc******************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.

 

Ra'ayi