Jan 25, 2018 17:13 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau  wasu dalilai ne na alkur'ani mai girma da suke tabbatar da shugabancin shugabanin shiriya na iyalan gidan Anabta tsarka? kafin amsa wannan tambaya sai a dakacemu da wannan.

************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa,domin neman amsar tambayar da muka bujuro da ita  za mu Ambato hakika ko kuma gaskiyar Alkur'ani mai girma  da a cikinta Allah ta'ala ya daukaka hikimarsa ta hanyar wakilta Annabinsa da ba ya  firta wata Magana da son ransa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka game da mahimin abu na bayyana tare da rarraba abinda yake a dunkule cikin alkur'ani mai girma Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Mun kuma saukar maka da alkur'ani don ka bayyana wa mutane abin da aka saukar musu don su yi tunanu) suratu Nahali aya ta 44.dalilin alkur'ani ya kasance dalilinsa na bayyanin anabta, kuma wannan shi ke tabbatuwa a kan ayoyi masu girma da ke kafa hujja na shugabancin shugabanin shiriya na iyalan gidan anabta tsarkaka amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya. Bayan Ambato wannan hakika ta alkur'ani, za mu bayyana cewa hakika Alkur'ani mai girma ya tattara ayoyi da dama da suke bayyani a game da shugabancin shugabanin shiriya na iyalan gidan anabta tsarkaka ta hanyar mai gaskiya amincecce amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, daga cikin wadannan ayoyi fadar allah madaukakin sarki:(Ya Ku Wadanda kuka bada gaskiya, ku bi Allah ku kuma bi Manzo, da kuma majibinta al'amuranku, sannan idan kuka yi sabani game da wani abu, to sai ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa, idan kun kasance kun ba da gaskiya da Allah da ranar lahira, (yin) wancan shi ya fi alheri ya kuma fi kyakkyawar makoma) suratu Nisa'I aya ta 59 bayan wannan aya sai Allah madaukakin sarki ya cikar kamalar hujjar da wannan aya mai girma yana mai cewa:(Idan kuma wani labari ya zo musu na aminci (cin nasara) ko na tsoro (rashin cin nasara), sais u watsa shi (don su raunana zukatan muminai) da dai za su komar da shi (watsa labarin) zuwa ga Manzo ko kuma zuwa ga majibintan al'amura daga cikinsu , lallai da wadanda suke tace shi (labarin) daga cikinsu sun gane shi(labarin da ya kamata su watsa). Da ba don falalar Allah ba a gare ku da kuma rahamarsa, da ba shakka kun bi shaidan(kan abinda yake kawata muku na miyagun abubuwa) in ban da 'yan kadan daga cikinku.) suratu Nisa'I aya ta 83, masu saurare hakika malimai sun kafa dalili cikin bincikensu na akida game da ayar (majibinta al'amura) wajen tabbatar da samuwar shugaba ma'asumi cikin ko wani zamani da yi masa biyayya da da'a, yiwa Allah da ma'aikinsa ne biyayya da da'a, kuma ya kasance makomar al'umma wajen magance sabani gami da jayayya domin shi magajin ilimin Annabawa ne, kuma ya kasance mai bayar da ra'ayi wajen gano hakika da gaskiyar Alkur'ani mai girma ya kuma bayyanawa mutane.

Hakika Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa shugabanin shiriya 12 na iyalan gidan anabta tsarkaka sune majibinta al'amura da aka Ambato cikin wannan aya, kamar yadda gaskiyar tarihi ya shaida cewa tabas amincin Allah ya tabbata a gare su su kadai ne aka kebance da tsarkakar isma tare da kuma mafi sanin littafin Allah Alkur'ani mai girma, a tsahon tarihi babu wanda yayi da'awar hakan, za mu nakalto muku wasu daga cikin wadannan riwayoyi, amma kafin hakan bari mu saurari wannan.

********************Musuc**************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na karamin sani kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai fara da riwayar da Shekh Saduk ya ruwaito cikin littafin Kamaluddin wa tamamu ni'ima, daga babban sahabin nan Jabir bn Abdullahi Ansari ya ce: (yayin da Allah madaukakin sarki ya saukar da wannan aya ga annabinsa Muhamadu dan abdullahi (s.a.w.a) :(Ya Ku Wadanda kuka bada gaskiya, ku bi Allah ku kuma bi Manzo, da kuma majibinta al'amuranku,..)sai na ce ya ma'aikin Allah mun san Allah da ma'aikinsa, su wane ne kuma majibinta al'amura wadanda aka daidaita yi musu biyayya da yiwa Allah da ma'aikin biyayya? Sai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce: sune Khalifofina Ya Jabir-kuma shugabanin musulmai bayana na farkonsu Abi Talib, sannan Hasan, sannan Husaini, sannan Aliyu bn Husaini, sannan Muhamadu bn Ali da aka fi sani cikin Attaura da Bakir, kuma za ka riske shi ya Jabir, idan ka hadu da shi ka meka gaisuwa ta zuwa gare shi, sannan Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ci gabada cewa sai Sadiku ja'afaru bn Muhamad, sannan Muhamadou bn Musa, sannan Aliyu bn Musa, sannan Muhamad bn Ali, sannan Aliyu bn muhamad, sannan Hasan bn  Ali, sannan mai sunana, da kuma mai elkunya irin nawa hujjar Allah a doron kasa ibn Hasan bn Ali, wannan shine wanda Allah ta'ala zai bude ambatonsa a hanunsa, daga gabashin kasa da yammacinta, wannan shi ne zai yi gaiba ga mabiyansa da masoyansa gaibar da ba za a tabbatar da fadar shugabancinsa face wanda Allah ta'ala ya jarabci zuciyarsa da Imani.Jabir ya ce: sai na ce Ya ma'aikin Allah shin mabiyansa za su amfana da gaibar ta sa? Sai ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce na rantse da wanda ya tayar da ni da anabta tabbas za su haskaka da haskensa kuma za su amfana da wulayarsa cikin gaibarsa, kamar yadda mutane ke amfana da rana, ko da kuma giragizai sun lullubeta, Ya Jabir wannan na daga cikin tabbaceccen sirrin Allah kuma ajiyar ilimin Allah, ina boye shi face ga ahlinsa).

Masu saurare, hakika an ruwaito hadisai da dama cikin litattafai masu inganci da suke tabbatar da cewa shugabanin shiriya 12 na iyalan gidan anabta tsarkaka sune tabbaci na majibinta al'amura da Allah ta'ala ya daidaita da'arsu da da'ar ma'aikin Allah (s.a.w.a), kwatamkwacin wannan hadisi ya kai hadin tawaturi, kuma hakika maliman da suka gabata kamar Hafiz Alhazaz daga cikin manyan maliman hadisi na karni na hudu  ya tattara hadisai masu inganci cikin littafinsa mai suna Kifayatu Asari fil A'imatul-Isnay ashara, kamar yadda maliman da suka biyo baya kamar Ayatollah Shekh Lutufullah a-ssafi ya tattara hadisai da za su kai 270 daga litattafai da dama masu inganci cikin littafinsa mai suna Muntahabul-Asari fil Imamu sani ashara) a game da wannan maudu'I, bayan hadisan da ya tattara cikin littafin Akabtu Noor, da Mulhakatu Ihkakul-Haq da sauransu wadanda suke haifar da tabbaci gami da yakini na ilimi na tabbacin majibinta al'amura da aka Ambato cikin wannan aya su ne shugabanin shiriya na iyalan gidan anabta tsarkaka amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya.a shiri  na gaba kuma za mu nakalto muku wasu riwayoyin a game da wannan maudu'I da yardar Allah madaukakin sarki.

**************************Musuc******************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.

 

 

Ra'ayi