Mar 28, 2016 14:16 UTC

Matasa a Jamhuriya Nijar sun koka kan yadda ake gindaya masu wasu sharidodi kafin daukan su aiki, alhaki a kasashen ketare inda suke zuwa bida ana daukan su ayukan ba tare da fuskanatar wani dogon bincike ba.

wannnan al'amarin a cewar wasu matasan yakan fusata da dama daga cikin su, har ma suyi watsi da neman aikin.

kazalika matasan sun koka kan yadda sai an nemi takardun kwarewa akan ayukan.

saidai hukumomin kasar sun ce suna iyakacin nasu kokari wajen samawa matasan ayyukan yi musamen a arewacin kasar data fuskanci tawaye a shekarun baya.

Tags