Apr 09, 2016 03:47 UTC

A yau shirin zai dorawa ne kan wanda ya gabata inda muka maida hankali akan ranar yaki da cutar tarin huka ta duniya, wace MDD ta ware domin kara fadakar da jama'a kan illolin wannan cutar da nufin kawar da ita a doron duniya. Taken ranar ta bana dai shi ne '’Kawar da Tarin Fuka a Rayuwata'’.

Shirin dai a yau na zanem ci gaban wanda ya gabata ne inda muka hankali kan ranar yaki da cutar tarin huka ta duniya, wace MDD ta ware domin kara fadakar da jama'a kan illolin wannan cutar da nufin kawar da ita a doron duniya. 

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kimanin kashi daya cikin uku na al'ummar duniya na dauke da kwayar cutar da ke haddasa ta. 

Cutar Tarin Fuka (TB, wato tuberculosis) ta dade tana addabar bil-Adama.

Ciwon yana haddasa tari, fitar da majina da jini da rama; wanda sananin wannan ciwo, miliyoyin mutane ne suke rasa rayukansu.

A makon daya gabata idan ana tune muna tare da Dr Attahir Sallah na sashen kula da masu fama da cutar dake a jihar Maradin jamhuriya Nijar, wanda yayi muna bayani kan cutar dama hanyoyin kamuwa da ita

A yau kuma zai dora muna ne kan illar cutar, dama hadarin boye cutar ga sauran jama’a


Tags