Apr 09, 2016 03:58 UTC

A yau shirin zai kaimu Najeriya inda wasu matasan kasar ke mayarwa da gwamnatin tarayyar martini akan cewa ita dama bata yi alkawarin bayar da tallafin Naira dubu biyar-biyar ba ga matasan kasar marasa ayyukan yi, a zaman cika alkawarin yakin neman zaben da dan takarar neman shugabancin kasa a jam`iyyar APC, kuma a yau shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya yi wa matasan.

A Najeriya,  wasu matasan kasar na mayarwa da gwamnatin tarayyar martini akan cewa ita dama bata yi alkawarin bayar da tallafin Naira dubu biyar-biyar ba ga matasan kasar miliyan 25 marasa ayyukan yi, a zaman cika alkawarin yakin neman zaben da dan takarar neman shugabancin kasa a jam`iyyar APC, kuma a yau shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya yi wa matasan.

Makasudin yin wannan alkawari da yunkurin cika shin dai baya rasa nasaba da irin halin rashin ayyukan yi da akasarin matasan kasar ke fama dashi.

Anyi amana cewar rashin aiki yi ga matasa a wannan kasa ya taimaka sosai wajen tursasawa matasan kasar aikata ayyukan da suka sabawa zamantakewar al’umma, irin su tada kayar baya da fashi da makami da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fasa bututu don satar man fetur da dangogin ayyukan ta`addanci da suka zama ruwan dare a wannan kasa.

A bara ne dai gwamnatin Najeriya ta bakin ministan matasa da wasannin na kasar, Solomon Dalong ya sanar cewa jam’iyyar mai mulki zata bayar da tallafin Naira dubu biyar-biyar ga matasan kasar marasa ayyukan yi daga farkon shekara 2016, saidai a cikin wannan ne a wani abu da ake wa kyallon tayi amai ta lashe gwamntin ta ce sam ita batayi wannan alkawari ba, lamarin da ya tayar 

Tags