Apr 25, 2016 13:02 UTC

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka amako, shrin da kan duba wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana a cikin mako a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, inda za mu leka tarrayar Najeriya, J. Nijar, Ghana, da dai sauransu, gwargwadon yadda llokaci ya ba mu hali, da fatan za akasance tare da mu.

Bari mu fara daga tarayyar Najeriya, inda a cikin wannan mako ne aka kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS ta gudanar da zamnata a babbar hedikwatarta da ke Abuja fadar mulkin Najeriya, inda ta zabi sabon shugabanta da sauran kanan kwamishinoni, wanda akan yi duk bayan shekaru 4.
Dan rahotonmu a Abuja Muhammad Sani Abubakar ya halrci ga kuma rahoton da ya aiko mana.
…………………….
To dangane da wannan batu na zaben sabon shugaban kungiyar ta ECOWAS, mun ji ta bakin Malam Nyumsu Jumro wani masani kan harkokin siyasar Afirka, kuma daya daga cikin jagororin kungiyoyin farar hula a Nijar daga birnin yamai, ya yi was ashen Hausa Karin haske kan yadda yake kallon wannan zabe.
…………………………..
Dangane da matsalolin da ake fama da sun a karancin man fetur a tarayyar Najeriya, hakan ya yi tasiri a cikin harkokin jama’a na yau da kullum a bangarori daban-daban, wanda hakan ne ma ya sanya dalibai a jami’ar Lagos suka yi wani bore, saboda sun ce rashin man yana cutarsu da kuma karatunsu matuka ta fuskoki da dama, wanda kuma boren nasu ne ya kai ga har aka rufe wannan jami’a. Malam Nuraddin Garba wani mazaunin birnin ne na Lagos, ya kuma yi sashen Hausa Karin bayani kan hakikainin abin da ya faru.
………………………………
To wannan matsala ta karancin man fetur a Najeriya dai ba ta tsaya  acikin kasar ba, domin kuwa tana shafar hatta kasashen da suk makwaftaka da Najeriya wadanda sukan samu mai daga kasar. Wasu daga cikin masu shigo da mai a jahar Damagarm ta J. Nijar ta barauniyar hanya, sun yi wad an rahotonmu Musa Malam Karin bayani kan yadda wannan lamari ya shafe su kai tsaye.
Ga abin da wani daga cikinsu yake cewa dangane da wannan matsala ta man fetur  a Najeriya.
………………………
To jama’a masu saurare kuna tare da mu ne a cikin wannan shiri na Afirka a Mako, daga muke gabatar muku daga sashen Hausa na muryar Jamhuriyar muslunci ta Iran.
Har yanzu dai muna nan kan batun Najeriya, a wannan karon kan batun badakalar da ake yi tsakanin shugaban kasar da kuma ‘yan majalisa kan batun kasafin kudin shekara ta 2016, wanda ‘yan majalisar suka ce sun yi dukkanin gyare-gyaren da ya kamata  acikinsa bayan da shugaban kasa ya mayar musu da shi a kwanakin baya, kuma suka sake mayar masa da shi, amma har yanzu shugaba Buhari bai sa hannun kan wannan kasafin kudi ba, inda yake sake binsa dalla-dalla.
Kan wannan batu, mun ji ta bakintsohon gwamnan jahar Kaduna da ke Najeriya, Alh, Balarabe Musa kan yadda yake kallon wannan batu.
………………………
A cikin wannan mako ne aka gudanar da zaben shugaban kasa  a kasar Chadi, wanda alamu ke nuni da cewa dai ga alama shugaba Idris Debi ne zai lashes hi.
Shugaba Debi dai yana fatan yin wa’adin mulki na biyar a kasar, bayan yak washe shekaru 26 yana kan karagar mulki, bayan da ya kwaci mulkin ta hanyar juyin mulki.
A nasu bangaren bangarorin adawa sun zargi gwamnati da tafka gagarumin magudi, inda suka ce suna manyan shedu kan hakan.
Kafin gudanar da zabukan dai ‘yan sanda sun yi amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Njamina da ma wasu yankuna, wanda suke adawa da salon mulkin Idris Deby, da suke bayyana shi da kama karya.
………………………….
A can kasa Ghana kuwa Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar ce ta sanar da cewa za a gudanar da wasu sauye-sauye a cikin dokokin zaben kasar.

A wata sanarwa da shugabar hukumar zaben kasar ta Ghana Charlotte Osei ta bayar  ta tabbatar da cewa hukumar ta amince za ta gudanar da wasu sauye-sauye a cikin dokokinta.
 
Osei ta kara da cewa kotun kolin kasar ce ta bukaci da a gudanar da wadannan sauye-sauye, kamar yadda kuma wasu daga cikin jam'iyyun siyasa na kasar sun bayar da irin wannans hawara.
 
A ranar Alhamis da ta gabata ce dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a birnin Kumasi na jahar Ashanti, inda suka nuna rashin amincewa da wasu ka'idoji na hukumar zabe, tare da yin kira da canja wasu dokokin kafin lokacin gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Nuwamban karshen wannan shekara.
……………………………………

Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Ghana ta sanar da cewa za a gudanar da wasu sauye-sauye a cikin dokokin zaben kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xin-huwa daga birnin Akra ya bayar da rahoton cewa, a wata sanarwa da shugabar hukumar zaben kasar ta Ghana Charlotte Osei ta bayar jiya Juma'a, ta tabbatar da cewa hukumar ta amince za ta gudanar da wasu sauye-sauye a cikin dokokinta.
 
Osei ya kara da cewa kotun kolin kasar ce ta bukaci da a gudanar da wadannan sauye-sauye, kamar yadda kuma wasu daga cikin jam'iyyun siyasa na kasar sun bayar da irin wannans hawara.
 
A ranar Alhamis da ta gabata ce dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a birnin Kumasi na jahar Ashanti, inda suka nuna rashin amincewa da wasu ka'idoji na hukumar zabe, tare da yin kira da canja wasu dokokin kafin lokacin gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Nuwamban karshen wannan shekara.

 …………………
A can Jibouti ma kan batun zaben ne, inda  ‘yan adawa a kasar suka kalubanci zaben shugaban kasar da Ismail Omar Guelleh ya lashe da gagarimin rinjaye.

Shugaban kasar Ismail Omar Guelleh , wanda yake shugabancin kasar tun shekara ta 1999 ya sake lashe zaben kasar da aka gudanar a ranar Juma’a, shi ne karo na hudu jere da yake lashe zaben, inda a wannan karo ya lashe zaben  kashi 86.68% na yawan kuriu da aka jefa, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.

Yan adawa dai na cewa an yi aringizon kuri'u, sanan an hana dayewa daga cikin wakilansu shiga runfunan zabe.

Dama kafin hakan wasu daga cikin jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi shugaban kasar da tauye 'yan cin jama'a, tun bayan da ya dare kan kujerar shugabancin kasar a shekara ta 1999.

…………………………………

To jama’a masu saurare lokacin da muke da shi dai ya kawo jiki a na za mu dakata sai Allah ya kai mu mako nag aba, za  a ju mu dauke da wani jigon, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum


Tags

Ra'ayi