Apr 27, 2016 15:00 UTC

Kamar sauran bangarorin al'umma kasar su ma matasan nijar ba'a bar baya ba wajen bayyana fatan su ga sabuwar gwamnatin kasar.

A jamhuriya Nijar bayan rantsar da shugaban kasar Alhaji Mahamadu Isufu a wani wa'adin shugabancin kasar karo na biyu al'umma kasar kasar ke bayyana fatan su, su ma matasan kasar ba'a bar su a baya ba domin dayewa daga cikin su na cewa kwaliya bata biya kudin sabulu danganeda shafe masu hawaye akan matsalolin dake ci masu tuwo a kwarya a wa'adin mulki Isufu na farko, don haka suke cewa ya kamata gwamnatin a wannan karo ta waiwaye su da idon rahama a wannan sabuwar majalisar ministoci mai mambobi 40.

Tags