Jun 04, 2016 07:13 UTC

A shirin ''Don matasa'' na wannan mako mun baiwa matasan Najeriya damar tofa albarkacin bakin su, kan cika shekara guda da kama ludayin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari

A Najeriya A yayin da wannan sabuwar gwamnati ta cika shekara guda da fara mulki, yau shirin na don matasa na jin ra’ayoyin matasa ne akan kamun ludayin gwamnatin Muhammadu Buhari da sauran abubuwan da suke ci masu tuwo a kwarya.

Shugaba Buhari dai yayi alkawarin yaki da matsalar tsaro dake zamen karfen kafa ga kasar, da yaki da cin hanci da rashawa sai kuma batun samarwa da matasa aikin yi.

To akan wannan batun ne shirin ya maida hankali, kuma a cewar dayewa daga cikin matasan kasar har yanzu fa da sauren rina a kaba dangeda alkawuran da gwamnatin tayi musu, duk da cewa wasu sun ce gwamnatin tayi iyakacin kokarinta akan abunda ya shafi tsaro.

saurari shirin domin jin karin bayyani