-
Nijar : An Samu Raguwar Mace-Mace Sanadin Cutar AIDS
Dec 02, 2018 17:48A Nijar, adadin mutanen dake mutuwa sanadin kamuwa da cutar AIDS/SIDA, ya ragu da kashi 15% daga shekara 2012 zuwa 2016, kamar yadda hukumomin kiwan lafiya na kasar suka sanar.
-
Boko Haram : Kasashen Yankin Tafkin Chadi Sun Bukaci Taimakon Duniya
Nov 30, 2018 03:36Kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru, sun bukaci taimakon kasashen duniya a yakin da suke da kungiyar Boko Haram.
-
'Yan Ta'adda Sun Sace "Yan Mata 15 A Jamhuriyar Nijar
Nov 25, 2018 11:50Majiyar hukuma daga garin Toumour da ke yankin Diffa da ke kudu maso gabacin kasar ta tabbatar da cewa; 'Yan 'ta'adda 50 ne su ka kai hari a cikin dare inda su ka yi awon gaba da 'yan mata 15
-
Nijar : Boko Haram Ta Kashe Ma’aikatan Man Fetur 7 A Diffa
Nov 22, 2018 12:23Rahotanni daga jamhuriya NIjar na cewa wasu ‘yan bindiga da ake dangata cewa na kungiyar Boko Haram ne, sun kashe ma’aikatan kamfanin Foraco 7 da ke aikin hakar rijiyoyin mai a garin Toumour da ke jihar Diffa a gabashin kasar.
-
Jirgin Faransa Marar Matuki Ya Fado A Nijar
Nov 18, 2018 10:09Rahotanni daga Jamhuriya Nijar na cewa wani jirgin sojin Faransa marar matuki ya fado a wajajen kauyen Bugum dake a yankin Torodi, kusa da birnin Yamai.
-
Yan Ta'adda Sun Kashe Jami'an Tsaron Kasar Niger Biyu A Kusa Da Kan Iyaka Da Kasar Burkina Faso
Nov 18, 2018 06:42Mahukuntan Niger sun sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da harin wuce gona da iri a yankin da ke kusa da kan iyaka da kasar Burkina Faso, inda suka kashe jami'an tsaron kasar biyu.
-
'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga A Nijer
Nov 12, 2018 08:04Gungun jam'iyun 'yan adawa a jamhiriyar Nijer sun gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna adawa da kundin zaben kasar
-
Nijar : Za'a Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Mai Aiki Da Hasken Rana A Yamai
Nov 05, 2018 11:14A wani mataki na shayo kan matsalar wutar lantarki a Yamai, babban birnin kasar, gwamnatin Nijar, ta cimma wata yarjejeniya da abokan huldarta domin gina wata tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana.
-
Bazum: Sojojin Nijar Na Kaddamar da Farmaki Kan Sansanonin 'Yan Ta'adda
Nov 03, 2018 19:13Ministan harkokin cikin gida na jamhuriyar Nijar Bazum Muhammad ya bayyana cewa, sojojin kasar suna kaddamar da farmaki a kan sansanonin 'yan ta'adda a yankunan da ke kan iyakoki a kudu maso yammacin kasar.
-
Tattalin Arzikin Nijar Zai Habaka A Shekara 2019
Nov 03, 2018 06:28Wani rahoto da asusun bayar da lamani ta duniya (IMF) ta fitar ya nuna cewa tattalin arzikin kasar Nijar zai karu da kashi 1,3% a shekara 2019 mai zuwa.